✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Farashin kaya ya tashi a Kano

Bayan ayyana dokar hana fita ta tsawon mako guda da gwamnatin jihar Kano ta yi, al’ummar jihar sun yi fitar dango don yin sayayya a…

Bayan ayyana dokar hana fita ta tsawon mako guda da gwamnatin jihar Kano ta yi, al’ummar jihar sun yi fitar dango don yin sayayya a kasuwanni.

Aminiya ta lura cewa jama’ar sun fi mayar da hankali wajen yin sayayyar kayan abinci da na masarufi da na bukatun yau da kullum.

Yawancin mutanen da Aminiya ta tattauna da su a Kasuwar Tarauni da Kasuwar Rimi da babban shagon Sahad sun bayyana cewa sun fito yin sayayyar ne don dai su samu abubuwan da za su yi amfani da su a wannan lokaci da aka rufe mutane a cikin gida.

Har ila yau al’umar jihar sun nuna takaicinsu game da yadda suka samu farashin kayayyaki a kasuwannin, inda ya yi tashin gwauron zabi, yayin da suka dora alhakin hakan akan ’yan kasuwa.

A cewar wata baiwar Allah, Hajiya Nana Aminu, duk da ta sayi kayayyakin da take bukata, yadda ta samu farashin yana bata mata rai.

“Kamar yadda kika sani ni na fi yin sayayya a karshen wata amma a yanzu mun zazzago asusunmu mun shigo don  sayayyar kayan abinci. Mun sayi shinkafa, mun sayi mai, mun sayi wasu kayayyakin, amma fa ba a kan farashin da muka saba saye ba,” inji Hajiya Nana.

Abin mamaki

Hajiya Nana ta kara da cewa, “Babbar jarkar man gyada muna sayenta N12,000, amma a yanzu ta koma N14,000.

“Haka sukari muna saye N16,000, amma a yanzu ya zama N18,000.

“Amma ni ina dora alhakin hakan a kan ’yan kasuwa. Yaya za a ce daga jin za a rufe gari ’yan kasuwa su kara farashin kayayyakinsu? Da a ce sun je saro kayan ne aka samu farashin ya karu to da sai su canza nasu farashin.

“Wani abu mai ban mamaki a yanzu idan kina son abu da yawa ma ba za su sayar miki ba saboda suna so su boye, sai nan gaba sun fito da shi su kara masa kudi,

“A gaskiya mu talakawa mu ne matsalar kanmu da kanmu. Amma sai a koma gefe a rika zagin shugabanni.” In ji Hajiya Nana Aminu.

Har ila yau Hajiya Nana ta yi kira ga shugabanni musamamn zababbu da su fito, su raba wa talakawa tallafi domin rage musu radadin da zaman gida zai iya jefa su.

“Wannan tallafi da gwamnati take rabawa ta fito ta fadada shi ta kuma yi shi a bude kowa ya zo ya bi layi ya karba, kamar yadda ake kada kuri’a. Ban yarda a ce a ba wani kudi ya raba ba, gaskiya kowa a ba shi kudinsa ko tallafinsa a tafin hannunsa”.

‘Talaka na bukatar dauki’

Shi ma wani bawan Allah mai suna Ibrahjim Shahrukhan ya bayyana cewa lamarin na rufe garin abu ne da ba zai zo da sauki ba musamman ga talaka,  don haka ya yi kira ga masu hannu da shuni da su kawo wa jama’a dauki na kayan abinci da sauransu.

Wata mai suna Salma Muhamamd kuma ta bayyana cewa duk da babu kudi a hannunta, haka nan ta fito domin yin sayayyar kayan amfanin yau da kullum.

“Ba ni da kudi a hannuna, amma saboda wannan doka da aka sanya ya zama dole na je na nemi rance domin yin ‘yar sayayyar kayayyakin da za mu bukata a gidan tsawon wanann lokaci”, inji ta.

Kowa da kiwon da ya karbe shi

Sai dai yayin da wani yake kuka, wani kuma murna yake.

Wani dan kasuwa, Alhaji Kabiru Mai Mai, wanda aka fi sani da KB, ya bayyana cewa a wannan lokaci ya yi cinikin da ya dauki tsawon lokaci bai yi irinsa ba,

“Kafin wannnan lokaci ba ma samun ciniki sosai. A rana bai fi na sayar da jarka daya ba, amma a ranar Laraba kawai na sayar da mai kimanin jarkoki 20.”

Al’umar jihar dai sun yi fatan gwamnati za ta kawo musu dauki domin rage radadin da dokar hana fitar za ta iya jefa su musamamn ma a wanann lokaci da watan azumi ke kusantowa.

Ranar Alhamis ne dai dokar, wadda aka ayyana bayan samun karin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus, za ta fara aiki da nufin hama ta yaduwa a cikin al’umma.