✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Gidajen rediyo da talabijin 40 za su durkushe

Akwai yiwuwar rufe gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu har 40 a Arewa matukar ba a kai musu dauki ba. Kungiyar Masu Gidajen Rediyo…

Akwai yiwuwar rufe gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu har 40 a Arewa matukar ba a kai musu dauki ba.

Kungiyar Masu Gidajen Rediyo da Talabijin Masu Zaman Kansu na Arewa ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Sanarwar mai dauke da sa-hannun Shugaban Majalisar Zartarwar kungiyar Alhaji Ahmad Tijjani Ramalan ta ce raguwar da aka samu ta kudin shiga sakamakon matsin tatttalin arzikin da annobar coronavirus ta haifar ce za ta sa kafofin yada labaran su rufe tashoshinsu baki daya.

Kungiyar ta kuma ce akwai ma’aikat 40,000 da ke aiki a wadannan gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu a arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya, kama daga ’yan jarida zuwa injiniyoyi da akanta-akanta da jami’an gudanarwa.

Sanarwar ta kuma ce kashi 80 cikin 100 na masu kallon talabijin ko sauraren rediyo a Arewa wadannan kafofin yada labaran 40 suke kallo ko saurare.

Masu kafofin yada labaran sun ce da ma ko kafin zuwan COVID-19 rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya suke kasancewar babu wasu manyan masana’antu a yankin.

Kungiyar ta kara da cewa tuni ta rubuta takarda zuwa ga Kungiyar Gwamnonin Arewa tana rokon a kawo wa tashoshin dauki kafin lokaci ya kure.

Annobar coronavirus dai ta durkusar da harkoki da dama a fadin duniya da ma Najeriya, lamarin da ya kai ga mutane da dama na fargabar rasa ayyukansu.