Da Dumi Dumi

COVID-19: Majinyata kusan 2000 sun warke a Najeriya

Injiniyoyin NCDC ne ke aikin kafa sabbin dakunan bincike da kuma kula da wadanda ake da su

Adadin masu jinyar COVID-19  da suka warke a Najeriya sun doshi 2,000, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu ya haura 6,400

Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter sun nuna cewa mutum 6,401 ne jimillar wadanda gwaji ya nuna sun kamu, yayin da aka sallami mutum 1,734 bayan sun warke, 192 kuma suka riga mu gidan gaskiya.

Hukumar ta kuma kididdige sabbin majinyatan da aka samu a ko wacce jiha, kuma kididdigar ta nuna cewa 131 a jihar Legas suke, sai 25 a Ogun, 15 a Filato, 11 a Edo.

A jihar Kaduna kuma an samu mutum bakwai, yayin da aka samu shida a Oyo, sai biyar-biyar a Adamawa da Yankin Babban Birnin Tarayya.

Sauran jihohin su ne Jigawa da Ebonyi da Borno masu mutum hurhudu, Nasarawa mai mutum uku,  sai Bauchi da Gombe  masu biyu-biyu.

ADVERTISEMENT

A jihohin  Enugu da Bayelsa  an samu mutum guda ko wacce.

Jihar Legas ce dai ke da kaso mafi tsoka na wadanda suka kamu da mutum 2,755, sai jihar Kano na biye mata da 842, Yankin Babban Birnin Tarayya kuma na rufa musu baya da 427.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya