✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘COVID-19: Mun ba kanmu tallafin biliyan N1.5’

Majalisar Dattawa ta bankado yadda aka yi watandar Naira biliyan 3.14 a hukumar yankin Neja Delta da sunan tallafin COVID-19. Binciken facakar biliyan N40 a…

Majalisar Dattawa ta bankado yadda aka yi watandar Naira biliyan 3.14 a hukumar yankin Neja Delta da sunan tallafin COVID-19.

Binciken facakar biliyan N40 a hukumar da kwamitin majalisar ke yi ya gano wani ma’aikacin hukumar ya samu Naira miliyan goma shi kadai, wasu mutum biyu kuma miliyan bakwai-bakwai a matsayin tallafin COVID-19, baya ga miliyan N475 da ta ba wa ‘yan sanda domin sayen takunkumi da sunadarin wanke hannu.

Daga cikin ma’aikatan NCDC, “Mutun uku sun samu miliyan biyar-biyar, mutum 148 miliyan uku-uku, mutum 157 miliyan N1.5 kowannensu, wasu 497 miliyan daya-daya, sannan wasu 464 Naira 600,000 kowannensu”, inji shugabar kwamitin na wucin gadi, Sanata Olubunmi Adetumbi.

Kwamitin na binciken hukumar ne bisa zargin wa-ka-ci-ka-tashi da Naira biliyan 40 wanda daga ciki aka ce an kashe biliyan 3.14 a kan tallafin COVID-19.

Amma Manajan Darektan hukumar na riko Kemebradikumo Pondei ya shaida wa kwamitin cewa an ba ma’aikatan tallafin Naira biliyan 1.5 ne domin rage musu radadin annobar, a matsayin wakilan jama’ar jihohin yankin Neja Delta guda tara

“Mun yi amfanin da kudaden ne wurin kulawa da kanmu. A matsayinmu na NDDC dole ne mu ma mu kula da kanmu”, inji shi.

Game da Naira miliyan 475 na sayen takunkumi da abun wanke hannu na ‘yan sanda kuma, Kemebradikumo ya ce bangarorin biyu na aiki tare ne kuma, “Mun samu bukatar hakan ne daga hukumar ‘yan sanda kuma hukumar gudanarwa ta amince a bayar.

“Mun ba su kudin amma ba su ba mu bayanin yadda suka kashe kudaden ba.

Ya kara da cewa, “an ba wa matasa tallafi domin rage musu radadin annobar saboda kada su tayar da rikici.

“An ware naira miliyan biyar-biyar ga mata da matasa da nakasassu a kowace mazabar dan majaliar dattawa”, inji shi.