Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
COVID-19 ta kashe shugaban kungiyar likitoci

Daya daga cikin dakunan binciken NCDC inda ake gwajin cutar coronavirus

COVID-19 ta kashe shugaban kungiyar likitoci

Cutar COVID-19 ta yi ajalin tsohon shugaba Kungiyar Likitoci na jihar Ondo, Michael Adeyeri.

Dakta Michael Adeyeri wanda ma’aikacin gwamnatin jihar ne ya rasu ne a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owo, daya daga cibiyoyin killace masu cutar.

Shugaban NMA mai ci, Dakta Wake Oke ya ce likitan ya rasu ne jin kadan bayan buba wani mara lafiya a asibitinsa.

Rahotanni sun ce mamacin ya kai kansa cibiyar kula da masu cutar COVID-19 da ke asibitin na Owo ne bayan ya lura cewa ya harbu da kwayar cutar.

Rasuwarsa na zuwa ne bayan cutar ta kashe kwamishinan lafiyan jihar, Wahab Adegbenro da mako guda.

SHi ma gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ya kamu da cutar a makon jiya, kafin daga baya ya warke.