✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta tsayar da harkokin Kannywood —Sanusi Oscar

Fitaccen darakta a masana’antar shirya fina-finai ta Hausa, Sanusi Hafeez, wanda aka fi sani da Sanusi Oscar 442 ya ce halin da masana’antar fina-finan Hausa…

Fitaccen darakta a masana’antar shirya fina-finai ta Hausa, Sanusi Hafeez, wanda aka fi sani da Sanusi Oscar 442 ya ce halin da masana’antar fina-finan Hausa da masu shirya fina-finan ke ciki ba abu ba ne mai dadi.

Daraktan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya ta wayar tarho, inda ya ce wasu daga cikinsu suna dogara da jagororinsu na siyasa ne a wannan halin da ake ciki.

“Magana ta gaskiya halin da ake ciki a yanzu ba hali ne mai dadi ba. Ita sana’ar Kannywood sai an fita ne ake samu.

“Tun da ba a fita, kuma yaya za a yi samu? Amma sai dai da yake hanyoyin Allah suna da yawa,” inji shi.

Wanda bai ajiye ba…

Daraktan ya kara da cewa, “mafi yawanmu idan ba ajiya ka yi ba, ai ba za ka dauka ba.

“Sai kuma wadanda suke da abin da za su yi, musamman ’yan siyasa wadanda a yanzu mafi yanwanci ’yan APC sun fi yawa, to sun samu tallafi daga jagororinsu.

“Amma mu da yake ba mu da mulki a hannunmu, ba ma tunanin wani abu, amma duk da haka mun samu tallafi, mun raba wa kowane dan Kwankwasiyya ko dan PDP buhun shinkafa.

“Mun samu tallafi daga jagoranmu na kwankwasiyya, Allah Ya saka masa.

“Amma halin da ake ciki ba mai dadi ba ne domin babu aiki, kuma sai an yi aiki ake samu.

“Kuma abin ya shammaci mutane, sai dai idan kuma ka tara ne. kuma ko ka tara ka kiyayi dokar kulle.”

‘Babu wani abu a kasa’

A game da shirye-shiryen da yake yi kuwa, Oscar cewa ya yi, “Babu wani abu da ake shirin yi domin yawancin wadanda ya kamata su ba da aikin, shi ma [dokar] kulle ta cinye masa jari.

“Ballantana dan kwadago, sai mutum ya jira tun da ba ka da jari.

“Sai jira kuma mu gani idan aka farfado a ci gaba da abin da ake yi. Amma dai a yanzu babu wani abu da ake jin dan Kannywood yana da karfin gwiwar zai yi.

“Sai dai kuma wasu abubuwa suna dan zuwa na tallace-tallaben COVID-19 da fyade da sauransu.”

A game da cutar ta COVID-19 kuwa, darakta Oscar ya ce Kannywood ta taka rawar gani ta hanyar wakoki da bidiyoyi domin wayar da kan al’umma.

A karshe ya yi kira ga jama’a da su dage da addu’ar Allah Ya kawo wa Najeriya shugabanni na gari.

“Su ma gwamnatin su ji tsoron Allah, su sani cewa wata rana za su mutu,” inji shi.