✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Trump ya kwanta a gadon asibiti

An garzaya da Trump asibiti kwana guda bayan kamuwarsa da cutar

An garzaya da shugaban Amurka Donald Trump zuwa asibiti kasa da sa’a 24 bayan ya kamu da cutar coronavirus.

Fadar shugaban ta White House ta ce an yanke shawarar garzayawa da shi asibitin sojoji na kasa da ke Walter Reed ne a matsayin kandagarki.

Shugaba Trump dai ya fara nuna alamun cutar ne ranar Alhamis, kafin daga bisani ya sanar da kamuwa da ita a ranar Juma’a.

Fadar shugaban ta ce alamun cutar sun riga sun bayyana a jikinsa, ko da yake har yanzu yanayin lafiyar tasa ba ta kai ga tabarbarewa ba.

Labarin kamuwarsa da cutar na zuwa ne wata daya gabanin zaben shugaban kasar inda zai fafata da dan takarar jam’iyyar Democrat, Joe Biden.

Rahotanni na nuna cewa Shugaba Trump na sanye da takunkumi lokacin da ya taka da kafarsa yayin fitowa daga fadar White House domin hawa jirgi mai saukar ungulun da ya kai shi asibitin a ranar Juma’a.

Asibitin sojojin da ke Walter Reed, mai makwabtaka da birnin Washington DC, shi ne inda galibi shugabannin Amurka ke zuwa domin neman lafiya.

Daraktar watsa labarai ta fadar White House, Alyssa Farah ta ce Mista Trump bai mika ragamar mulki ga mataimakinsa Mike Pence ba kafin tafiyar tasa.

A ka’idar kundin tsarin mulkin kasar, kamata ya yi shugaban ya mika ragamar shugabanci ga mataimakin nasa har zuwa lokacin da zai murmure ya dawo bakin aiki.