✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Yadda kananan sana’o’i ke fuskantar barazanar rushewa

Masu matsakaita da kananan sana’o’i a fadin Najeriya sun shiga halin tsaka mai wuya tun bayan da gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi suka kafa…

Masu matsakaita da kananan sana’o’i a fadin Najeriya sun shiga halin tsaka mai wuya tun bayan da gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi suka kafa dokar zaman gida a kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Dokar, wadda ta hana tafiye-tafiye a tsakanin jihohi ta yi matukar tasiri a kan kananan ‘yan kasuwa wadanda a halin yanzu suke fuskantar barazanar durkushewar sana’o’insu baki daya.

Wani mai sayar da kayan wayoyin hannu a Abuja, Gabriel Shima, ya bayyana cewa akwai yiwuwar wasu kayayyakin wayoyin wadanda ya karbe su bashi ba za su samu shiga ba saboda har sun fara lalacewa.

A nashi bangaren, Shuaib Abdullahi, wanda yake kiwon kifi, ya ce sana’arsa ya tsaya cak sannan ya koka da yadda farashin abincin dabbobi ya tashi.

Wata mai kamfanin samar da abinci, Grace Uzorka, ta ce ta shiga halin matsi saboda wahalar da take fama da ita wajen samun kayan abincin.

‘Masana’antu sun tsaya’
Kwararru sun bayyana cewa halin da kasar ta shiga ya sa masana’antu da yawa sun dakatar da aiki a sassa da dama na Najeriya.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Kanana da Matsakaitan Sana’o’i na yankin Arewa ta Tsakiya, Injiniya Auwal Ibrahim Bununu, ya ce halin da cutar coronavirus ta jefa masana’antu na tilasta musu rufe ayyukansu zai yi mumunan tasiri a kan tattalin arzikin kasar.

Masu shagunan sayar da kayan waya sun koka cewa kayayyakin da suka sayo ka iya lalacewa

A nata bangaren, jami’ar tsare-tsare a kungiyar mata masu kanana da matsakaitan sana’o’i ta Najeriya, Mis Nancy Nathaniel, ta ce rage kudin ruwa da kashi 5 cikin 100 ga kananan sana’o’i da Babban Bankin Najeriya (CBN) zai yi, zai taimaka sosai wajen kawar da matsalolin da kananan sana’o’in suke fuskanta.

Shugaban Kungiyar Masu Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Kasa (NASME), Degun Agboade, ya bukaci bankin na CBN da ya samar wa masana’antun agajin kudaden da za su taimake su su ci gaba da ayyukansu.

Yadda al’amura suke a jihohi
Kanana da matsakaitan masana’antu a jihar Bayalsa sun koka da matsalolin da cutar coronavirus ta jawo wa sana’o’insu musamman dokar zaman gida da gwamnatin jihar ta sanya na tsawon mako daya da kuma rufe mashiga jihar, tashoshin mota, wuraren shakatawa, mashaya, da sauran wuraren taruwar jama’a.

Su kuwa masu kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Borno nemo hanyar bullewa suka yi.

In hagu ta kiya…

Aisha Musa Kida daga jihar ta Borno ita ce mai kamfanin Na’ish Kitchen a Maiduguri wacce take koyar da girki da samar da abinci.

Ta ce tun da aka fara fama da cutar coronavirus aikinta ya tsaya cak.

A cewarta, a maimakon harkar da ya saba, kamfaninta ta mayar da hankali wurin samar da kayayyakin kariya saboda tabbatar da cewa ba su dakatar da aiki ba.

Taimakon gwamnati

A jihar Oyo, kanana da matsakaitan masana’antu sun nemi gwamnatin tarayya ta taimake su da kudade saboda su samu farfadowa daga matsalolin da suka fada a dalilin halin da aka shiga.

Wani dan kasuwa a jihar, Chief Wale Oladoja, ya nemi gwamnatin da ta samar da basussuka wa kanana da matsakaitan masana’antun.

Masu gidajen cin abinci ma sun kusa cinye jarin saboda abin ya shafe su

A nasu bangaren, kanana da matsakaitan sana’o’in a jihar Abia sun nemi gwamnatin jihar da ta sassauta musu haraji.

Wasu daga cikinsu sun bukaci gwamnatin ta dauke musu biyan haraji da kuma samar musu da basussuka da za su yi amfani da su wurin farfado da sana’o’insu.

Harkar intanet

Masana’antu sun koma harkoki ta intanet a Kaduna.

Wata mai sayar da kayan kwalliya, Nabila Usman, ta ce tana sauya yanayin aikinta zuwa intanet, inda take kai wa masu siya har gidajensu.

Ta ce tana amfani da shafukan sada zumunta na WhatsApp wurin gudanar da sana’arta.

Su kuwa masu kanana da matsakaitan sana’o’i a Legas farashin kayayyaki suka kara.

Wani ma’aikacin samar da burodi a jihar, Ajao Ismail, ya ce kamfanoni da yawa sun dakatar da ayyukansu dalilin dokar zaman gida; hakan ya sa kayan da ake amfani da su wurin gasa burodin suka kara kudi.

Ya bayyana cewa hakan ya tilasta wa kamfanin nasu kara kudin burodin.