✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: ‘Yan Najeriya 317 sun dawo daga Birtaniya

‘Yan Najeriya 317 ne Gwamnatin Tarayya ta kwaso daga kasar Birtaniya bayan bulllar annobar COVID-19 ta hana su baro kasar. Sanarwar da gwamnatin ta fitar…

‘Yan Najeriya 317 ne Gwamnatin Tarayya ta kwaso daga kasar Birtaniya bayan bulllar annobar COVID-19 ta hana su baro kasar.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce kananan yara guda tara na daga cikin wadanda suka dawo din.

A ranar Lahadi ne Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa 175 daga cikin fasinjojin sun sauka ne a Abuja, kafin jirgin ya karasa Legas ya sauke sauran 142 din.

Ministan wanda ya ce jirgin ya samu jinkiri saboda wasu dalilai, ya kara da cewa dukkannin wadanda suka dawo din za su killace kansu na kwanaki 14 kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara domin tantance cutar COVID-19.