✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Yawan wadanda suka kamu ya karu da 248

A Najeriya, an samu karin mutane 248 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a sa’o’i 24. Alkaluman baya-bayan nan da Hukumar Yaki da…

A Najeriya, an samu karin mutane 248 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a sa’o’i 24.

Alkaluman baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar sun nuna cewa hakan ya kawo jimillar wadanda suka kamu a kasar zuwa 4,399.

Bayan sanar da wani gyara a lissafinta na daren 9 ga wata, hukumar ta ce zuwa tsakar daren Lahadi adadin wadanda aka sallama ya tashi 778, yayin da wadanda suka mutu suka kai 143.

“A daren 9 ga watan Mayu mun sanar da sallamar mutum 45 da rasuwar mutum biyu a Yankin Babban Birnin Tarayya.

“Saboda tangardar na’ura mun yi kuskuren sanar da sallamar mutum 32 da mutuwar mutum biyu.

“Don haka [hakikanin adadin shi ne] an sallami mutum 13 a Yankin Babban Birnin Tarayya, mutum biyu kuma sun riga mu gidan gaskiya a ranar 9 ga watan Mayun 2020”, inji NCDC.

Galibin sabbin majinyatan dai, wato 81, a jihar Legas suke, 35 a Jigawa, 26 a Borno, 20 a Bauchi.

Sai kuma Yankin Babban Birnin Tarayya mai mutum 13, Edo 12, Sakkwato 10, Zamfara kuma bakwai.

Jihohin Kwara da Kebbi na da mutum hurhudu, Taraba da Ogun da Ekiti na da bibbiyu, yayin da Osun da Bayelsa ke da guda-guda.

A cikin mutum 4,399 din da suka kamu zuwa yanzu dai jihar Legas ce ke da 1,845, sai Kano na biye mata da 602, sannan Yankin Babban Birnin Tarayya mai 356.