✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cristiano Ronaldo ya zura akalla kwallo 15 a shekara 14 da suka wuce

Bayan wasan da Juventus ta lallasa Parma 2 da 1 a wasan Gasar Serie A ta jiya Lahadi, Cristiano Ronaldo ya sake kafa wasu tarihin.…

Bayan wasan da Juventus ta lallasa Parma 2 da 1 a wasan Gasar Serie A ta jiya Lahadi, Cristiano Ronaldo ya sake kafa wasu tarihin.

Ronaldo ne ya zura kwallo biyu, wanda hakan ya sa mai shekara 34 ya samu samu jimillar kwallo 16 a kakar bana.

Bayan kwallon da ya zura a ragar Parma, ya kasance ya zura kwallo a wasa 7 a jere ga Juventus a Gasar Serie A, wanda tun shekarar 2005, ba sake samun hakan ba sai bana.

Wasu dai suna ganin kamar Cristiano Ronaldo ya zufa, ganin cewa shekarunsa 34, kuma saura kwanaki kadan ya cika shekara 35, amma kullum lamarinsa kara gaba yake yi duk da cewa akwai sauyi a yanayin wasansa, wanda bai rasa nasaba da shekarun.