✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar COVID-19: Yadda kasuwa ta bude wa masu kemis-kemis

A yayin da cutar COVID-19 ta karade duniya, ciki har da Najeriya, cutar ta kassara al’amura da yawa, ta kawo cikas ga tattalin arziki da zamantakewa da…

A yayin da cutar COVID-19 ta karade duniya, ciki har da Najeriya, cutar ta kassara al’amura da yawa, ta kawo cikas ga tattalin arziki da zamantakewa da kiwon lafiya. Ko yaya al’amarin yake a bangaren masu kemis-kemis da sayar da magunguna? 

Aminiya ta binciko yadda al’amarinsu yake.

A Jihar Katsina, lokacin da ake zaman kulle, doka ta samar da sassauci kan sayar da kayan abinci da magunguna.

Ciniki ya karu sosai

Alhaji Saifullahi na daga cikin masu kantunan sayar da magani a Katsina, kuma ya shaida wa Aminiya cewa, “Lallai an samu ciniki sosai fiye da shekarun baya da babu coronavirus, domin cinikin ya ninka kusan sau uku ko hudu a rana. Sannan mafi yawan magungunan da aka rika saye su ne na mura da zazzabi. Na manyan cututtuka sai kadan ake saye.

“Sai dai wata matsalar da aka samu ita ce, kayan in mun je saye sai mu tarar an kara kudi kuma ga karancinsu. In mun kawo, kuma mai saye kuka saboda abin ya yi masa tsada.

“In ka nuna masa halin da ake ciki, sai ya riga ka fadin coronavirus ta hana neman komai. Wani ma bashi zai nema kuma dole ka ba shi, lura da halin da yake ciki”, inji shi.

‘Asibitoci sun raja’a kan coronavirus’

Shi kuwa wani da aka sakaya sunansa, cewa ya yi dalilin raja’ar mutane zuwa shagunan sayar da magunguna shi ne, “In ka je asibiti sai a yi ciwo daban magani daban.

Kila ciwon ciki ne ya damu mutum ko hawan jini wanda mutum ya dade da shi, amma kawai sai a ce awon coronavirus, karshe a ce an killace mutum; bayan kuma ba cutar da ya je kanta ke nan ba. Hatta ko mura mutum ba ya yi balle a ce akwai alamun coronavirus”, inji shi.

Shi kuwa Malam Kabir Bala ya ce ya je Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Katsina a kan ciwon gyambon ciki da zafi amma sai aka yi masa awon coronavirus.

Maimakon ya ga sakamakon gwajin sai kwatsam ya ga sunansa ya fito a cikin mutum tara da aka ce sun kamu da cutar a Katsina.

“Amma kuma ba a kira ni ba balle a ce ga halin da nake ciki, balle abin da za a yi mini har zuwa yau”, inji shi.

‘Hukumomin lafiya sun yi gum’

Duk wani yunkuri na jin ta bakin hukumomin kiwon lafiya a kan kin zuwan mutane asibiti a wannan lokaci, abin ya ci tura.

Sai dai wata majiya ta ce su kansu asibitocin sun tsayar da karbar marasa lafiya in ba wadda ta kai kololuwa ba, sai masu cutar ta COVID-19 kawai. Majiyar ta ce sun kuma dauki wannan mataki ne domin dakilewa da hana yaduwar cutar.

Harkar magunguna ta ja baya a Jos

A Jihar Filato, yayin da mutane da dama ke ganin masu shagunan sayar da magunguna harkokin kasuwancinsu na tafiya sosai a wannan lokaci na annobar coroanvirus saboda yadda marasa lafiya da dama ba su zuwa asibiti, binciken da wakilinmu ya gudanar a garin Jos, ya gano cewa masu shagunan sayar da magunguna suna cikin mawuyacin hali na rashin ciniki.

A zantawar da ya yi da wakilinmu kan wannan al’amari, Shugaban Masu Shagunan Magunguna na Kasuwar Dilimi da ke Jos, Alhaji Muhammad Usman ya ce kasuwar magunguna yanzu ba ta tafiya, domin komai ya tsaya.

Ya ce “Yanzu idan ka je asibiti za ka samu babu mutane, haka idan ka je wajen masu sayar da magunguna a kemis, nan ma babu mutane.” Ya ce wata matsalar kuma yanzu ita ce, farashin magunguna duk sun karu.

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin wadanda suke tafiyar da harkokin babban shagon sayar da magunguna na Gali Phamacy da ke garin Jos, Sagir Abdulkadir Ahmed cewa ya yi “Gaskiya harkar cinikin magunguna abubuwa sun canja, ciniki ya koma baya.

“Wasu magungunan ma ba a samun su saboda an kulle wurare, wasu magungunan da dama farashinsu ya karu. Don haka cinikinmu ya ja baya sakamakon wannan annoba ta corona.”

Ya ce kafin zuwan wannan annoba suna ciniki sosai a shagonsu, saboda a Jos da sauran jihohin Arewa kamar Gombe da Bauchi da Nasarawa da Adamawa da Taraba da kuma Abuja duk suna kiran su a waya su sayi magani a tura musu. Amma ya ce a yanzu ba su samun masu sayen magungunan.

A zantawarsa da wakilinmu, Sunusi Kabir Nalele na shagon sayar da magunguna na Nalele Phamacy da ke garin Jos, cewa ya yi tun daga lokacin da annobar COVID-19 ta zo, harkokin sayar da magunguna ta yi baya.

A cewarsa, yanzu mutane ba su zuwa sosai kamar kafin a samu annobar. Haka kuma ya ce an samu karin farashin magunguna saboda rashin shigo da kaya, daga kasashen waje.

Mutane na gudun zuwa asibiti a Maiduguri

A Jihar Borno kuwa, masu shagunan sayar da magunguna a Maiduguri sun shaida wa Aminiya halin da suka samu kansu a ciki a fannin ciniki da ba da magunguna ga marasa lafiya da ke kauce wa zuwa asibiti, gudun kada a ce sun kamu da cutar.

Malam Isa Karube da ke da shagon sayar da magunguna na Al-Amik ya ce hakika sun samu masu zuwa ganin likita a wurin nasu da kuma sayen magani.

Ya ce akasarin masu zuwa sukan yi korafin cewa ba su son zuwa asibiti ne, gudun kada a ce sun kamu da cutar coronavirus. Ya ce idan sun zo sukan sayar musu da magani daidai irin rashin lafiyar da suke da ita.

Ciniki ya karu, amma magunguna sun yi tsada

Isa ya kara da cewa sun samu cinikin magani fiye da kowane lokaci kuma magunguna sun kara kudi saboda dokar kulle, kamfononi ba su aiki kuma motoci masu daukowa daga Legas ko Fatakwal da Enugu ko Kano sun ninka kudin mota.

“Hakan ya sa dole muka kara kudin magungunan,” inji shi.

Malam Idris da ke shagon sayar da magunguna na Jumail da ke hanyar Baga, cewa ya yi “Gaskiya an dan samu abin da aka samu, ba yabo ba fallasa amma magunguna sun kara kudi, duk da cewa ba kowanne karin kudin ya shafa ba kuma zan iya cewa mun samu marasa lafiya da yawa da suke zuwa a duba lafiyarsu kuma su sayi magani su koma gida.

“Akasarin masu zuwa idan ka ce su je asibiti, sukan nuna ba su son zuwa, sun gwammace su zo nan a ba su magani.”

Abind a ya sa marasa lafiya gudun zuwa asibiti

Wani marar lafiya da wakilinmu ya ci karo da shi a wajen sayen magani, Muhammad Rabi’u ya bayyana wa Aminiya cewa tun bullar cutar ya kaurace wa zuwa asibiti, domin ya ce sun taba kai matar yayansa tana fama da laulayin ciki amma sai aka ce za a yi mata gwajin coronavirus.

Ya ce tun daga wancan lokaci ya tabbatar babu amfanin ya sake zuwa asibiti, har sai al’amura sun yi sauki game da cutar coronavirus.

Ita kuwa wata mata da Aminiya ta samu a daya daga cikin shagunan magunguna, Maryam Kingi ta ce “Na zo sayen magani ne, don a yanzu da zarar ka je asibiti karshe za a ce ka kamu da cutar corona.

“Don haka gara in zo in sayi magani, idan har ba cuta ta yi tsanani ba. Don wani zazzabi, mura ko tari da ciwon kai, nakan zo shago in sa yi magani in koma gida kuma Allah cikin ikonSa nakan warke.”

Me ya hana asibitoci karbar marasa lafiya?

Wata likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ta ki amincewa ta bayyana sunanta, ta shaida wa Aminiya cewa hakika ana kin karbar marasa lafiya, amma hakan bai rasa nasaba da yajin aikin da likitoci suke yi a lokacin. Ta ce a yanzu da yake an dan samu sauki, al’amuran sun daidaita.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin babban mai kula da harkar magunguna a asibiti kwararru na jihar amma ya ci tura saboda har zuwa hada rahoton nan wakilinmu ba ya samun sa a ofis.

Mutane sun tagayyara a Ibadan

A Jihar Oyo, binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa farashin magani ya tashi a shagunan sayar da magani a Ibadan.

Hakan ya biyo bayan kin karbar majinyata da wasu asibitoci suka rika yi ne a wannan lokaci da cutar ta dabaibaye kasa.

Binciken ya nuna cewa akwai da yawa daga cikin majinyatan da suka tagayyara har da rasa rayuka a dalilin rashin karbar su a asibitoci da tsadar magani a shagunan sayarwa.

Daya daga cikin irin mutanen da suka tagayyara, Ustaz Tahir Zubairu ya ce “A gaskiya ba mu rasa ran kowa daga cikin iyalina ko na kusa da ni ba, amma mun sha tsadar magani a lokacin da mai dakina ta haihu.

“Babu yadda za mu yi, dole ne mu nemi maganin da za a ba ta da zai taimaka wajen murmurewarta da jaririnta.”

Shi kuwa Tola Oyeniyi, wanda direban mota ne, cewa ya yi ’ya’yansa biyu suka kai wasu asibitoci uku (an sakaya sunayensu), da aka ki karbarsu.

“Sai wani likita makwabcina ya yi iya kokarin ceto rayukansu ta hanyar rubuta sunayen maganin da suka rika saya da tsada, ba tare da nasara ba domin yarar sun rasu a lokuta daban-daban.

Aminiya ta tuntubi wadansu masu shagunan sayar da magani a Ibadan, inda suka yi gum da bakinsu saboda tsoro.

Sabon salo: Kemis a faranti a Ibadan

Haka kuma akwai mata da ke dauke da magungunan sayarwa a kawunansu suna yawo a gidajen matan aure suna sayarwa, bayan an fada musu irin ciwon da ke damun mutane, ba tare da awon likita ba.

Irin wadannan mata suna sayar da magani ne a boye ba tare da izinin hukuma ba.

Wani mai kantin sayar da magani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Dole mu kara kudin magani domin a wannan lokaci babu hanyar tafiya zuwa sayo magungunan.

“Wadansu daga cikin mutanenmu suna yin kasadar tafiya wasu garuruwa su samo maganin da tsadar gaske, wanda dole su sayar da tsada domin cin riba”.