✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar kansa ce ta biyu wajen halaka mutane – Dokta Zainab Shinkafi

Gidauniyar Medicaid da ke yaki da cutar kansa  ta bayyana cewa cutar ce ta biyu wajen hallaka mutane a duniya. Shugabar Gidauniyar kuma Uwargidan Gwamnan…

Gidauniyar Medicaid da ke yaki da cutar kansa  ta bayyana cewa cutar ce ta biyu wajen hallaka mutane a duniya.

Shugabar Gidauniyar kuma Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Bagudu Shinkafi ce ta bayyana haka a yayin bikin zagayowar Ranar Yaki da Cutar Kansa da aka ware don fadakarwa a kan cutar a ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata.

Dokta Zainab Bagudu ta ce kididdiga ta nuna cewa kimanin mutum dubu 250 ne cutar ke hallakawa duk shekara a sassan  duniya. Ta ce kungiyar Medicaid wadda ta kafa kimanin shekara 12 da suka gabata, za ta ci gaba da ayyukanta na fadakarwa da tallafa wa masu cutar kasancewar an yi mata rajista kuma tana hulda da kungiyoyin duniya inda take samun tallafi.

Ta ce akwai bukatar karin azama wajen fadakar da al’umma kan cutar ta hanyar nuna wa jama’a amfanin yin gwaji a kan cutar a kai-a kai don shawo kanta kafin ta kai mataki mai muni da ke da wuyar magancewa.

Ta ce daga cikin nasarorin da kungiyarsu ta samu akwai ta kafa cibyoyin yin rajista a kan cutar da bada horo ga malaman jinya da gudanar da tarurruka da yin gwaji kyauta da kuma taimaka wa masu cutar wajen jinyarta.

Ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan ware wasu kudade a kasafin kudin badi don kafa asibitoci 6 a yankuna 6 na kasar nan da za su maida hankali a kan magance cutar kansa.

Taron na wuni biyu ya kunshi zantawa da ’yan jarida a ranar Juma’a a ofishin hukumar da ke Abuja, sai kuma ranar Asabar inda aka yi tattaki na kilomita 5 don fadakar da al’umma da zaburar da su.

Babbar Mai taimaka wa Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya Hajo Sani ta wakilci Hajiya A’isha Buhari a yayin tattakin wanda ya samu halartar fitattun ’yan fim na Nollywood da Kannywood da tsohon Kyaftin din Super Eagles na Najeriya, Peter Rufa’i.