✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: Gwamnan Legas ya kai ziyarar ba-zata filin jiragen sama

A wannan mako kasashen duniya da dama sun kara karfafa matakan kariya don kauce wa yaduwar cutar Kurona, inda a Najeriya ma mahukuntanta suke kara…

A wannan mako kasashen duniya da dama sun kara karfafa matakan kariya don kauce wa yaduwar cutar Kurona, inda a Najeriya ma mahukuntanta suke kara karfafa matakan kare yaduwar cutar. A Jihar Legas inda aka samu wata ’yar Najeriya da ta kamu da cutar ta shigo da ga kasar waje ranar 14 ga Maris da muke ciki, Gwamnan Jihar Legas Mista Babajide Sanwo-Olu ya kai ziyarar ba-zata a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas domin gane wa idanunsa irin matakan kariya da ake dauka domin hana baki shigowa da cutar zuwa Najeriya.

A lokacin ziyarar ba-zatar Gwamnan ya ce ya je filin jirgin sama na Murtala Mohammed ne kasancewar shi ne hanyra shigowar jama’a mafi girma a kasar nan inda ake da kashi mafi yawa na bakin da ke shigowa ta wannan kafa  daga kasashen ketare. Ya ce don haka ya zama wajibi a tsaurara matakan kare yaduwar cutar daga wannan bangare.

A lokacin ziyarar tasa Gwamna Sanwo-Olu ya duba tare da yin nazarin yadda ake tantance mutanen da kan shigo kasar nan, ya kuma duba kayayyakin da aka tanada don yin aikin. Kayayyakin da suka hada da wajen da aka ware domin killace wadanda ake zargi da da cutar. Gwamnan ya ce a baya-bayan nan gwamnatin jihar ta rubanya yawan jami’an kiwon lafiya masu aikin ko-ta-kwana daga 30 zuwa 60 a filin jirgin saman. Ya ce mahukuntan kasar nan na daukar kwararan matakai domin kare yaduwar cutar.

Gwamnan Jihar Legas ya kai ziyarar ba-zatar ce a ranar Talatar da ta gabata a daidai lokacin da aka samu wata mace ’yar Nigeriya mai shekara 30 wacce ta kamu da cutar Kurona bayan ta shigo Legas  daga kasar Amurka a makon jiya.