Da Dumi Dumi

Cutar Kurona: Kayayyakin kariyar fuska da hannu sun yi karanci a kasuwannin Legas

Kayan kariyar Cutar Kurona

Tun bayan sanar da bullar cutar Kurona a Legas al’ummar jihar suke rububin sayan kayan kariya daga cutar lamarin da ya sanya kayayyakin da suka hadar da: Kyallan da ake amfani da shi wajen rufe fuska da rufe baki tare da hanci, sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin da safar hannu ta roba, duk sun yi karancin a kantuna da manyan shaguna da rumfunan sayar da magunguna.

Wakilan Aminiya sun kewaya wasu daga cikin wuraren da ake sayar da irin wannan kayayyaki a yankunan Surulere, Ikeja, Agege da Ogba inda suka tarar jama’a sun saye kayayyakin kariyar.

Wasu masu sayar da kayayyakin kariyar a manyan shagunan da manyan rumfunan magunguna sun shaidawa Aminiya cewa, da sanyin safiyar ranar Juma’a da misalin karfe 8 na safe jama’a suka yi cincirindon a kantuna suka saye kayayyakin kariyar.

Haka zalika, wasu masu sayar da kayayyakin a wasu manyan shaguna sun shaida karewar kayayyakin da misalin karfe 11 na safiyar yau Juma’a.

Zuwa yanzu dai al’ummar birnin Legas na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba, inda wasu ke sanye da kayan kariyar baki da hanci da na hannu wasu kuma na harkokinsu a haka saboda karancin kayayyakin, yayin da hukumomi a jihar suka ce su tsaurara matakan hana yaduwar cutar ta Kurona.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya