✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: Majalisa ta tafi hutun dole na mako biyu

Majalisar Dokoki ta Kasa ta tafi hutun dole domin dakile yaduwar cuyat Kurona  da ke ci gaba da barazana ga duniya. Sai dai wannan mataki…

Majalisar Dokoki ta Kasa ta tafi hutun dole domin dakile yaduwar cuyat Kurona  da ke ci gaba da barazana ga duniya. Sai dai wannan mataki ya samu suka daga ’yan Najeriya da dama inda suka bayyana cewa hakan bai dace b.

A ranar Talata ce Majalisar Wakilai ta bayyana zuwa hutu na mako biyu don ba wakilan majalisar su yi gwaji kan cutar tare da yin cikakken shiri don dakile yaduwar cutar a zauren Majalisar Dokokin.

Kudirin rufe majalisar na mako biyu ya biyo bayan bukata mai taken: “Bukatar Gaggawa Don Dakile Yaduwar Cutar Kurona a Najeriya” da dan Majalisa Idem Uyime (PDP, Akwa Ibom) ya gabatar ne.

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Ndidi Elumelu (PDP, Delta) ya goyi bayan bukatar inda ya kara da cewa a rufe majalisar na mako biyu, inda wakilan majalisar suka amince ba tare da hammaya ba. Ya ce lokacin zai bayar da dama mahukunta majalisar su samar da hanyoyin rigakafin cutar.

“Ta yadda dukkanmu za a yi mana gwaje-gwaje. Wannan babban al’amari ne, domin ba ka san da wa kake musabaha ba,” inji shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa dan majalisa Isiaka Ibrahim ya nuna takaici ne kan yadda Najeriya ba ta da cibiyoyin dakile aukuwar cututtuka.

Shi kuwa dan majalisa Awaji-Inombek (PDP, Ribas) ya nuna rashin jin dadinsa ne kan yadda majalisar ta yi watsi da kudirin da ke neman a dawo da ’yan Najeriyar da suka makale daga China, inda ya ce, “yanzu abin da muke tsoro ya kama mu.”

Da yake magana kan kudirin dan majalisa Obinna Chidoka (PDP, Anambra) ya yi kira ne ga gwamnati ta samar da hanyoyin kariya da za su hana yaduwar cutar a kasar nan.

Ya ce,  baya ga asibiti babu inda jama’a suka fi zuwa irin Majalisar Dokoki ta Kasa, don haka sai ya yi kiran a dauki matakan da suka wajaba don hana yaduwar cutar a ginin majalisar. Chidoka ya kuma shawarci Gwamnati ta kakkafa karin cibiyoyin killace masu cutar, sannan ’yan majalisar su yi tsayuwar daka sosai wajen sanya ido don tabbatar da sashin lafiya yana gudanar da aikin da aka dora masa.

Da yake jagorantar muhawarar dan majalisa Uyime ya ce akwai bukatar shugabannin majalisar, su kafa kwamiti na musamman da zai hada hannu da hukumomin lafiya domin hana yaduwar cutar.

Ya ce, wajibi ne kuma Gwamnatin Tarayya ta sake karin kudi ga Ma’aikatar Lafiya da Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC), domin killacewa da jinya da dakile yaduwar cutar.

Kakakin Majalisar Benjamin Okezie Kalu a wata sanarwa a ranar Talata da daddare ya ce, za a iya sake duba matsayin majalisar.

Wakilanmu da suka zazzagaya harabar majalisar sun lura babu wani matakin kariya da aka dauka.

Tuni daidaikun mutane da kungiyoyin jama’a suka shiga Allah wadai da wannan mataki da majalisar ta dauka, inda suke cewa babu dalilin da za a rufe majalisar.

 

‘Babu sabuwa cutar a Najeriya’

Dan kasar China da aka killace bayan ya sauka daga jirgin saman kasar Habasha a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas gwaje-gwaje sun nuna ba ya dauke da cutar.

An ce dan kasar China ya rika yin tari a cikin jirgin, inda ana sauka aka mika shi ga jami’an kiwon lafiya na filin jirgin saman bayan an raba shi da sauran fasinjoji. Bayanai sun ce an sanya ido kan dan China kan yiwuwar kamuwa da cutar Kurona.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an gudanar da gwaje-gwaje a kansa inda sakamako ya nuna ba ya dauke da cutar. Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Leags ma ta tabbatar da haka a shafinta na tiwita.