Da Dumi Dumi

Cutar Kurona ta kama Ministan Lafiya a Iran

Ma'aunin cutar Kurona

Minista a Ma’aikatar Lafiya ta Iran ya kamu da cutar Kurona yayin da cutar ke ci gaba da bazuwa a kasar.

Adadin wadanda suka rasu bayan kamuwa da cutar ya kai mutum 16 a kasar Iran.

Akwai rahotannin da ke cewa adadin wadanda suka rasu ya zarta haka.

A birnin Kum na Iran ne cutar ta fara bulla wanda kuma birni ne  mai muhimmanci da mabiya Shi’a a fadin duniya ke zuwa ziyara a-kai-a-kai.

Haka an samu rahotannin bullar cutar da ake canja mata suna  Cobid-19 a kasashen Afghanistan da Iraki da Bahrain.

ADVERTISEMENT

A yanzu ana fargabar bullar cutar a sauran kasashen da ke makwabtaka ganin yadda matafiya ke baluguro a yankin.

…Za a shawo kan cutar

Shugaban Iran ya bukaci mutanen kasar su kwantar da hankalinsu yayin da ake kokarin dakile bazuwar cutar numfashi ta Kurona.

Shugaba Hassan Rouhani ya ce kasar za ta shawo kan cutar wadda ta kashe akalla mutum 16 a kasar.

Iran ta ce mutum 95 ne suka kamu da cutar ta Cobid-19 tun makon jiya amma ana tunanin adadin ya zarce haka.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce abin damuwa ne yadda ake samun karuwar cutar.

WHO ta ce za ta aike da magunguna da sauran kayan gwajin cutar ga Iran wadanda ake sa ran isarsu tun jiya Alhamis.

Shugaba Rouhani ya yi kira ga mutane su kiyaye shawarwarin da ma’aikatar lafiya ta ba su.

Zuwa yanzu an kiyasta cutar ta kama mutane fiye da dubu 80 a fadin duniya, tare da hallaka a kalla 2,700.

…Zarif ya yi kiran hada kai game da cutar Kurona

Ministan Harkokin Wajen Iran Jabad Zarif ya yi kiran a samar da hadin kan yankin wajen tunkarar cutar ta Kurona.

“Kamar dai sauran cututttuka – har da ta’addanci – #COBID19 ita ma ba ta san da kan iyakoki ba kuma ba ta tantance mutane da kabilarsu ko kuma addininsu,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

“Domin a yake ta, ba wai abu ne na ya kamata kawai ba. A’a lallai ne a kanmu mu yi haka, don haka ne Iran take kira a samu hadin kan kasashen yankin domin yakarta.” inji shi.

 

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya