Da Dumi Dumi

Cutar Kurona ta kama Ministar Sifaniya

Irene Montero

An killace Ministar daidaito ta kasar Sifaniya Irene Montero sakamakon kamuwa da tayi da cutar kurona tare da abokanan aikinta a ranar Alhamis.

A cikin wadanda aka killace akwai mataimakin Firayi Ministan kasar  Pablo Iglesias, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar.

“Ministar (Irene Montero) na cikin yanayi mai kyau yayin da Mataimakin Firayi Ministan Sifaniya Pablo Iglesias da wasu na ci gaba da zama a wajen da aka killace su, sakamakon yanayin cutar,” Kamar yadda aka sanar.

Rahoton na cewa, tun da safiyar Alhamis aka sanar da cewa duk mambobin Gwamnatin sai an yi masu gwajin cutar, daga bisani a fitar wa kowa da sakamakon gwajin da aka yi masa.

Mahukuntar kasar sun kira taron gaggawa sakamakon yaduwar cutar da nufin shirin hanyoyin dakile annobar.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya