Search
Subscribe
Cutar kwalara ta karu a Yobe da Borno

Cutar kwalara ta karu a Yobe da Borno

Rahotanni na bayyana cewa, akalla mutum 21 ne suka kamu cutar amai da gudawa a jihar Borno da kuma mutum tara a jihar Yobe kamar yadda hukumarlafiya ta duniya ta sanar.

Akwai alamar raguwar masu dauke da cutar a jihar Borno yayin da ake samun karuwar masu dauke da cutar a jihar Yobe.

Yankunan da suke dauke da cutar a Borno sun hada da kananan hukumomin Jere, Maiduguri, Konduga da Guzamala. Yayin da rahotan ya sanar da cutar a garin Gulani da yankunan shida na Damaturu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin