✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar kyanda ta barke a Jamhuriyyar Kongo

Akalla mutane fiye da1500 ne cutar kyanda ta halaka a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo tun daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, wanda mafi akasarinsu yara ne…

Akalla mutane fiye da1500 ne cutar kyanda ta halaka a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo tun daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, wanda mafi akasarinsu yara ne kanana ‘yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.

A cewar Ofishin Ministan Kiwon Lafiya na kasar ta Kongo, an samu barkewar cutar kyanda a wasu yankuna na kasar guda 23 daga cikin yankuna 26 na kasar a birane da karkara, inda akalla ake tsammanin kusan mutane 87,000 da ake zaton sun kamu da cutar tun farkon wannan shekara kawo yanzu.

Sai dai ana samun cikas wajen magance cutar a cikin kasar ta dalilin matsalar tsaro da kuma yadda harkokin  kiwon lafiya ke fuskanta karancin kayan aiki.

Bayan wadannan matsaloli, akwai batun rashin takamaiman tsare-tsare na yin rigakafi, ana kuma samun gazawa ko kuma yankewar rigakafi, haka shi kansa batun kula da magungunan cutar, saboda rashin ingantattun wuraren ajiya masu sanyi.

Ana shirya yaki da cutar ta hanyar tura lokitocin yankunan da kuma taimakon kungiyoyin agaji a fanin harkar  kiwon lafiya irin su Medecins Sans Frontieres.

Kungiyar ta ce tana yaki da yaduwar cutar kyanda, tare da hukumomin kiwon lafiya a yankuna 10 na kasar.

Yankunan da cutar ta fi kamari sun hada da Haut-Lomani, Lualaba, Tanganyika, Arewacin-Kibu, Kudancin-Kibu, Tshopo, Kasai, Kasai ta Tsakiyal, Haut-Uele da kuma Ituri.

Wata majiya ta kusa da hukumomin kasar ta bayyana Gidan Radiyon BBC cewa ana ci gaba da tattara kudaden da za su ba da damar shirya gangamin na rigakafi don kare yaduwar kwayoyin cutar zuwa cikin yankunan da cutar ba ta kai ba.

Sama da yara miliyan biyu ne suka samu rigakafin a watan Afrilun bana, wasu karin miliyan 1.4 za su samu cikin ‘yan kwanaki masu zuwa a yankunan da cutar ta riga ta bulla.