✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Cutar mantuwa ka iya zama ajalin ‘yan kwallo’

Akwai yiwuwar tsofaffi daga cikin ’yan wasan kwallo su kamu da cutar mantuwa da kashi uku da rabi kuma har ta kai su ga mutuwa…

Akwai yiwuwar tsofaffi daga cikin ’yan wasan kwallo su kamu da cutar mantuwa da kashi uku da rabi kuma har ta kai su ga mutuwa fiye da sauran jama’a, kamar yadda wani nazari ya nuna. Masana a Jami’ar Glasgow da ke   Ingila sun dade suna bincike kan fargabar da ake da ita cewa dukar kwallo da kai na iya raunata kwakwalwa. Nazarin ya fara ne kan abin da ake fargabar ya kashe tsohon dan wasan West Brom, Jeff Astle wanda aka alakanta da yawan samun matsala a kansa.

Nazarin ya kwatanta mutuwar ’yan kwallo 7,676 da kuma sauran mutum 23,000. Mutanen da aka yi amfani da su daga duniyar kwallo sun taka leda a kungiyar wasa ta Scotland a tsakanin 1900 da 1976. Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ce ta gabatar da nazarin ga duniya bayan dan tsaiko da nazarin ya samu sakamakon bata wa iyalan Astle rai da ya yi.

Sashin Hausa na rediyon BBC Hausa ya ruwaito, duk da cewa ’yan kwallo na da hadarin mutuwa sakamakon cutar mantuwa, amma zai wuya su mutu sakamakon matsalolin irin su cutar zuciya da cutar daji da matsalar huhu. Alakar wasanni da cutar mantuwa ta zamo abin muhawara a kai a fadin duniya a tsawon shekaru, har zuwa lokacin da aka fitar da wannan nazari.

To sai dai babu shaidar da ke nuna karuwar cutar mantuwa a tsakanin tsofaffi ’yan wasan kwallon kafa. Tsohon dan wasan kwallon Ingila, Astle ya samu cutar mantuwa inda ya rasu a 2002 yana dan shekara 59.

Binciken da aka gudanar game da rasuwar Astle ya nuna yadda bugun kwallo da kai ya haifar wa marigayin cutar damuwa. Sai dai wani bincike da Hukumar FA da PFA suka yi ya rushe wancan ikirari bisa abin da aka bayyana da tangardar na’ura.