Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Cutar murar tsuntsaye ta bulla a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sake bullar cutar murar tsuntsaye wacce a shekarun baya ta jawo asarar dubban kaji a jihar.
Daraktan Sashin kula Dabbobi na Ma’aikatar Ayyukan Gona na Jihar, Dokta Shehu Bawa ya shaida wa Aminiya cewa rahotannin da suke hannu a yanzu sun nuna cewa an samu bullar cutar a wasu gonaki uku a jihar.
Ya ce kuma tuni ofishinsa ya dauki samfurin ciwon ya aike da shi zuwa Cibiyar Bincike Lafiyar Dabbobi da ke bom a Jihar Filato don ci gaba da bincike.
Dokta Bawa ya ce, “Zuwa yanzu ba za mu iya cewa ga yawan kajin da cutar ta kama ba, saboda ma’aikatanmu suna kan aiki don gano haka. Kuma mun dakatar da kashe kajin har sai mun samu umarni daga Ma’aikatar Gona ta Tarayya.”
Dokta Bawa ya kara da cewa ma’aikatarsu ta fara shirya tarurrukan kara wa juna sani ga masu kiwon kaji kan hadarin cutar da alamominta da hanyoyin da za a bi wajen rigakafinta.
Da Aminiya ta tuntubi Shugaban kungiyar Masu Kiwon Kaji ta kasa Reshen Jihar Kano, Dokta Muhammad Auwal Haruna, ya bayyana damuwarsa kan bullar cutar ya ce kungiyarsu tana aiki kafada-da -kafada da Ma’aikatar Gona ta Jihar wajen dakile yaduwar cutar.
Ya nemi ’ya’yan kungiyarsu su ba gwamnati hadin kai ta hanyar yin biyayya ga dokokin gwamnati.

ADVERTISEMENT