Da Dumi Dumi

Cutar pneumonia ka iya kashe yara miliyan daya a Najeriya – MDD

Yara kusan miliyan 1.4 ne a Najeriya ka iya rasa rayukansu sakamakon cutar pneumonia mai alaka da sanyin yanayi a cikin shekara 10 masu zuwa, in ji Mjalisar Dinkin Duniya (MDD).

A wani rahoto da asusun yara na MDD wato Unicef ya fitar, ya yi hasashen cewa Najeriya ka iya fuskantar mafi yawan mace-mace a duniya, wanda cutar ta pneumonia za ta haifar.

Yara miliyan 6.3 ne Unicef ya yi hasashen za su mutu a duniya baki daya daga cutar.

MDD ta yi hasashen kasar Indiya ce ta biyu da za a fi samun mace-macen, sai kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da za ta iya zama ta uku.

Asusun yaran ya ce yara miliyan 9 ne za su mutu daga pneumonia da kuma wasu manyan cutukan idan har ba a dauki matakan riga-kafi ba.

ADVERTISEMENT

Unicef ya bayar da shawarar a kara yawan riga-kafin domin kauce wa mace-macen sannan kuma ya ce tuni Najeriya ta fara yin hakan.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya