✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da a kara albashi a rage ma’aikata da a bar karin wanne ya fi?

A ci gaba da rikita-rikitar samun matsaya tsakanin Kungiyar Kwadago da gwamnati a kan mafi karancin albashi, gwamnoni sun tabbatar da cewa lallai fa idan…

A ci gaba da rikita-rikitar samun matsaya tsakanin Kungiyar Kwadago da gwamnati a kan mafi karancin albashi, gwamnoni sun tabbatar da cewa lallai fa idan aka matsa sai sun kara mafi karancin albashi, to za su rage ma’aikata. Wannan maganar ta jawo cece-kuce da muhawara a tsakanin mutane, duk da cewa wasu daga cikin gwamnonin sun nuna cewa za su iya biyan albashin a haka. Amma wasu daga cikinsu kuma suna ganin a bar kowace jiha ta zabi abin da za ta iya biya. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin ra’ayoyin mutane, kuma ga abin da suke fada:

Na goyi bayan kara albashi a rage ma’aikata – Alhaji Rabiu idris Kaya

Daga Jamilu Adamu

Alhaji Rabiu Idris Kaya Sabon Gari Zariya: “Na goyi bayan kara albashi a rage ma’aikata. Dalili kuwa shi ne, idan ka duba halin da ma’aikatan kasar nan ke ciki, suna cikin mawuyacin hali saboda albashin na su ba ya isarsu kuma ma’aikatan ba sa samun albashinsu a kan lokaci kuma idan ka duba da kyau, ma’aikatan kasar nan abin tausayi ne sakamakon karancin albashi. Daga karshe ina bai wa gwamnoni shawara da su yadda da wannan karin kudin da Gwamnatin Tarayya ta zo da shi domin ba su da dalilin kin hakan.”

A dai samu daidaito – MWO Iro Mohammed Wada

Daga Aliyu Babankarfi, Zaria

MWO Iro Mohammed Wada: “Ni a ra’ayina ba karin albashin da zai jawo koran ma’aikata ake bukata ba, a samu daidaito shi ne ya fi dacewa. Kamar inganta rayuwar mutane da zai iya shafi kowa da kowa, mai aiki da mara aiki yadda kowa zai yi walwala da samun saukin rayuwa. Amma idan aka kara albashi aka kori ma’aikata, zai jefa wasu cikin kunci.”

Kara albashi na da kyau – Alhaji Kabir ’Yar’aduwa

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina

Alhaji Kabir ’Yar’aduwa: “A nawa ra’ayin karin albashin ya fi saboda zai kara wa ma’aikata hazaka wajen gudanar da ayyukansu. Kazalika, zai kara wa gwamnati kwar jini da kuma tabbatar da adalci. Karin albashin zai kara fadada tattalin arziki domin zai rage radadin rayuwa ga ma’aikata duk da cewa akwai fargabar tashin farashin kaya daga ’yan kasuwa wanda hakan bai kamata ba. Sannan kuma tilasta wa jihohi da kamfanoni biyan zai amfanar da jama’ar kasa baki daya.”

A kara amma kada a rage ma’aikata – Bashir Danlami

Daga Jamilu Adamu

Bashir Danlami: “Gaskiya ni na fi son a kara albashi saboda ya fi alheri. Idan ka rage ma’aikata zai jefa da dama daga cikin ma’aikatan cikin hali kaka-nika yi saboda suna da iyalan da ke karkashinsu.”

Yin karin ya fi dacewa – Alhaji Ibrahim Barde S/kasuwa

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina

Alhaji Ibrahim Barde S/kasuwa: “Idan aka duba ana daukar ma’aikaci ne daga karamin mataki. A hankali yana kara matsa wa gaba, hidimomi na karuwa kuma yana rayuwa da abin da bai taka kara ya karya ba. Har ta kai ga iyali sun fara taushe shi, karshe sai bashi ya fara haye shi saboda rashina wadataccen albashi. Amma wannan karin zai taimaka matuka. Kazalika, harkokin kasuwanci za su kara bunkasa da ma kasuwancin na yanzu ya dogara ne a kan ma’aikata. Saboda haka a kara masu albashin ya fi a rage su.”

Rage farashin kayan masarufi muke bukata –Sunusi Muhammad

Daga Aliyu Babankarfi, Zaria

Sunusi Muhammad: “Ba na goyon bayan karin albashin da zai sa a kori ma’aikata. A samu sulhu a nema wa al’umma saukin rayuwa. Misali rage kudin man fetur da kudin makaranta da asibiti da sauransu domin rayuwar karamin ma’aikaci ta inganta, ba wai a kara albashin da zai ja masa kora ba.”