✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da alama wani mai dauke da cutar kanjamau ya warke

An kasa gano cutar kanjamau (HIB/AIDS) daga jikin wani mutum mai dauke da cutar bayan da aka yi masa dashen sababbin kwayoyin halitta, kuma wannan…

An kasa gano cutar kanjamau (HIB/AIDS) daga jikin wani mutum mai dauke da cutar bayan da aka yi masa dashen sababbin kwayoyin halitta, kuma wannan ne karo na biyu da likitoci suka yi irin wannan gwaji.

A yanzu dai, marar lafiyar da ke zaune a birnin Landan wanda ake yi wa lakabi da ‘London Patient’ ya daina nuna alamun cutar tsawon wata 18 kuma ya daina shan magungunan cutar.

Sai dai masu bincike na ganin akwai sauran lokaci kafin a ce ya warke gaba daya.

Masana dai na ganin wannan wani mataki ne mai muhimmanci a gano maganin cutar kanjamau  kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wadansu masana daga jami’o’in Landan da Imperial da Cambridge da kuma Odford suka hada kai wajen yin wannan aiki. Wannan ne karo na biyu da wani mai dauke da cutar ya warke ta wannan hanyar.

Shekara goma da ta gabata, aka yi wa wani mai dauke da cutar dashen bargo daga wani wanda ba ya dauke da cutar a Berlin na kasar Jamus, wanda aka kira da ‘Berlin Patient’ a tarihin nemo maganin cutar.

Sinadarin CCR5 shi ne ke bai wa kwayar cutar kanjamu damar shiga cikin kwayoyin halittar dan Adam. Sai dai akwai ’yan tsirarun mutane a duniya da ba sa iya kamuwa da cutar kanjamau saboda ba a halicce su da sinadarin CCR5  ba. Ana yi wa mai dauke da cutar kanjamau dashen kwayoyin halitta daga mutumin da ba ya dauke da sinadarin CCR5.

An yi wa marar lafiyar na Landan dashen kwayoyin halitta daga jikin daya daga cikin irin mutanen da ba su da CCR5 kuma daga nan sai jikinsa ya gaza daukar kwayar cutar kanjmau din.

Sai dai ana iya samun kwayoyin cutar kanjamau din kadan a jikinsa, sai dai ba za su yi wani tasiri ba.

Farfesa Graham Cooke na Makarantar Nazarin Lafiya ta Birtaniya kuma mai nazari kan cututtukan da ake iya dauka a Kwalejin Imperial de ke Landan ya ce sakamakon wannan dashe ya kara masu kwarin gwiwa.