✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da ba domin barasa ba da na dara haka – Dharmendra

Jarumin Indiya, Dharmendra ya bayyana yadda barasa ta haifar masa da cikas a harkarsa ta fim.Dharmendra ya bayyana cewa a shekarun baya, ya kasance mai…

Jarumin Indiya, Dharmendra ya bayyana yadda barasa ta haifar masa da cikas a harkarsa ta fim.
Dharmendra ya bayyana cewa a shekarun baya, ya kasance mai yawan shan barasa, wanda dalili ke nan ma ya ta’allaka matsalolin da ya rika fuskanta a sana’arsa gare ta. Ya ce da ba ba domin ta’ammali da giya ba, da shahararsa ta fi da haka.
“Na dawo daga rakiyar shan barasa a yanzu, domin kuwa ita ce ummul aba’isin na matsalolina a baya.” Inji shi, a yayin da yake tattaunawa da ’yan jarida a birnin Delhi, a kokarinsa na tallata sabon fim dinsa mai suna ‘Yamla Pagla deewana 2.’
Jarumin dai a bana shekararsa 77 a duniya, amma yana cikin koshin lafiya, musamman ya ce ya bar shan barasa ne shekaru biyu da suka gabata. Kafin ya bar shan barasa, ya yi fama da laulayi iri daban-daban.
A ’yan kwanakin nan, babu abin da ya sa gaba sai tallata sabon fim dinsa, wanda a ciki ya fito a matsayin mai wasan barkwanci. A 2011 ne kashi na daya na fim din ya fito, a bana kuma ake shirin fitar da kashi na biyu. ’Ya’yansa biyu, Sunny Deol da Bobby Deol duk sun fito cikin fim din, abin da ke nuna cewa al’amarin nasu ya kasance tuwona-maina.
Ba wannan ne karo na farko da Dharmendra ya shirya fim tare da ’ya’yansa ba, domin kuwa a fim din ‘Apne’ ma ’ya’yan nasa ne suka mamaye shi. Dayake wannan fim bai samu gamsassar nasarar da aka zata ba, dalili ke nan a yanzu ya takarkare yana tallata martabarsa.