✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da da uwa da Fasto sun kashe budurwa

Sun yi farfesu da zuciyarta A farkon makon nan ne ’yan sanda a Jihar Ogun suka kama wani matashi da mahaifiyarsa da kuma wani Fasto…

  • Sun yi farfesu da zuciyarta

A farkon makon nan ne ’yan sanda a Jihar Ogun suka kama wani matashi da mahaifiyarsa da kuma wani Fasto bisa zargin kashe wata budurwa ’yar jami’a, inda suka cire zuciyarta da wasu sassan jikinta suka yi farfesu suka sha.

Haka kuma, bincike ya nuna cewa mutanen da ake zargi sun yi sabulun wanka da tokar wasu sassan jikinta da suka hada da kai da kafafu, duk a yunkurinsu na su samu abin duniya.

Aminiya ta zanta da wadanda ake zargin, a inda ake tsare da su a Sashin Kula da Manyan Laifuffuka (CID) na Rundunar ’Yan sandan   Jihar Ogun, inda Segun Philip, Faston da ake zargi da hada kai da sauran. ya  shaida mata cewa a garin Imesi na Jihar Osun yake zaune, kuma ya hadu da matashin mai suna Adeeko Owolabi, kimanin shekara biyu da suka gabata ta hanyar ’yar uwar mahaifinsa. Ya ce a kwanakin baya ne matashin ya kira shi ta waya, ya shaida masa cewa al’amura sun tabarbare musu, kasancewar mahaifinsu ya rasa aikinsa, haka mahaifiyarsu ta rasa nata, kwangilar da take samu tana kula da iyalinta ma yanzu ba ta samu. Shi ma ya ce ya samu matsalar jarrabawa a zangon karatunsa na karshe. Don haka ya bukaci Faston ya taimake su, ta yadda za su fita daga wannan kangi.

“Na fada masu cewa akwai aikin da zan yi musu su fita daga kangin amma aikin daga Littafin Attaura ne na Annabi Musa. Na ce su kawo Naira dubu 250. Sun samo rance suka kawo kudin sai na shaida musu cewa akwai wani lokaci da na yi irin wannan aikin ba a samu dace ba, don haka akwai wani aiki mai sarkakiya da zan yi musu, domin ina tsoron kada su yi asarar kudin da suka aro bukata ba ta biya ba,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Sai na fada wa yaron cewa aikin da zan yi musu a yanzu yana da wuya, domin ana bukatar sassan jikin mutum kuma ba zan yi amfani da mutum daga cocina ba, ana bukatar mutum daga nesa.”

Faston ya ce, “Sai Adeeko ya ce ba damuwa, muddin za su samu biyan bukata, su warware matsalolinsu. Sai ya kira budurwar ta waya, ya tura mata kudi, ya ce ta same shi a otel a Jihar Osun. Bayan ta zo sai ya yaudare ta, ya ce zai kai ta wajen dan uwan mahaifinsa. Da ta amince sai ya kawo ta cocina, inda kafin su karaso na umarci iyalina su shiga can cikin cocin su yi barci. Na ce musu kada wanda ya fito, domin zan yi aiki na musamman ne. Koda ya iso da yarinyar dare ya fara yi, misalin karfe 8 na dare, domin cocin nawa na nesa da gari ne, a cikin kungurmin daji yake. Da suka iso, yarinyar ta gaji sai ya ce za ta kwanta. Na ba shi shimfida ya yi mata, ni kuma na ba su waje. Sai ya zo ya ce min ta yi barci.

“Na ce masa mu hakura mu kyale yarinyar nan, sai matashin ya dage cewa sai an yi aikin, domin su fita daga matsalar talauci da ke addabarsa da iyalinsa. Nan sai ya dauki tabarya ya kwada mata a ka, take ta mutu, ni kuma na sanya wuka na cire kanta da nunowanta da hannuwanta, na cire zuciyarta da wasu sassan cinyarta, wadanda da su ne na hada maganin. Na shirya miyar farfesu ta musamman da zuciyarta da kuma yankin naman akuya da muka saya, muka yi abinci muka rabar sadaka. Sannan na babbake kan da kafafun da hannu, inda na dauki kashi guda na tokar, na yi wa mahaifiyar yaron sabulun wanka da shi, kashi guda kuma muka sadaukar ga abin bauta, yayin da kashi na uku muka hade shi a cikin miyar da na yi wa mahaifiyar yaron,” inji Faston.

Fasto Segun Philip ya bayyana wa wakilinmu cewa ya yi nadamar aika-aikar da suka yi, wadda ya ce ba su yi nasara ba, domin ba su samu kudin ba bayan da suka kammala aikin kuma sun kasance cikin nadama da dimuwa tun kafin a kama su.

“Na samu kwarin gwiwar yin aikin ne domin idan an yi nasara ni ma za su taimaka min in samu kudin da zan gyara cocina, domin ina cikin bakin talauci kuma da katako na gina cocina,” inji shi.

A nasa bangaren matashi mai shekaru 23, Adeeko Owolabi ya shaida wa Aminiya cewa halin da iyayensa suka shiga na rashin aiki ne ya sanya ya ga ya kamata ya yi wani abu domin fitar da su daga matsala. Ya ce sun hadu da budurwar mai suna Fabour Daley Iladele a Jami’ar Legas, kimanin wata biyu da suka gabata.

“A ranar da abin zai faru ce na kira ta a waya, na ce ta same ni a otel. Na kwatanta mata inda za ta same ni. Na ce ta hau motar zuwa Ibadan daga unguwarsu a Mowe a Jihar Ogun. Daga nan sai ta hau mota zuwa garin Ikere. Lokacin da ta same ni a otel ta fada min cewa a gajiye take, za ta huta. Sai na yi mata karya na ce ta zo mu je wajen yayan babana. Daga nan ne na kai ta cocin, inda nan ma ta ce ta gaji za ta kwanta. Bayan da na yi mata shimfida a kasa, da na lura ta yi barci sai na dauki tabarya na buga mata a kai, inda Fasto Philip ya zo ya cire kanta da hannuwanta da nonuwanta da zuciyarta da sassan cinyarta; wadanda ya hada maganin da su, yayin da muka zubar da ragowar jikin a wata tsohuwar rijiya, na dauki kasa na rufe,” inji shi.

Ya ce, “Ni ban ci miyar da aka yi da zuciyar yarinyar ba, domin ba ni aka hada wa maganin ba. Kamar yadda na fada, iyayena nake so a yi wa asirin, domin su yi kudi mu fita daga talauci. Wannan ne ya sanya na dauko iyayen nawa daga Legas, muka je Jihar Osun muka kama otel. Ni a cocin nake kwana amma mahaifina da mahaifiyata na kwana a otal, sai dai suna zuwa cocin a yi musu addu’a.”

“Bayan an yi wa mahaifina tasa addu’ar, an yi masa wankan addu’a sai Faston ya sallame shi ya koma Legas, yayin da mahaifiyata ta ci gaba da zama domin a karasa mata nata. Da aka hada farfesun zuciyar yarinyar, mahaifiyar tawa ba ta sani ba, ta dauka naman akuya ne, domin ta ga lokacin da muka sayo akuya muka yanka. Mun kai mata miyar da aka hada da sassan jikin yarinyar a otel dinta, inda ta ci,” inji shi.

Adeeko ya ce, “Na yi nadamar wannan abu da na aikata, ina dab da zuwa hidimar kasa ke nan bayan na kammala karatun jami’a, sai ga shi na saka kaina cikin wannan hali. Kirana ga ’yan uwana matasa shi ne, su kula cewa babu yadda za a yi mutum ya yi kudi ta irin wannan hanya, domin komai yana da lokaci.”

Ya ce ya yi hakan ne a yunkurinsa na fitar da mahaifansa daga kangin talauci.

A nata bangaren, mahaifiyar yaron mai suna Bola Adeeko ta shaida wa Aminiya cewa ba ta da masaniyar cewa miyar da aka hada mata ta sha da sassan jikin mutum aka yi ta. Ta ce ta nufi cocin ne domin a yi mata maganin matsalolin da suka addabi iyalinta amma ba ta san cewa irin wannan aiki aka shirya yi mata ba.

“Dana ne ya kai ni wajen Faston amma sun yi min rufa-rufa, domin ba su fayyace mini lamarin ba, domin da na san haka ne ba zan yarda ba. Ta yaya zan yi amfani da dan wani domin in yi arziki, bayan ni ma dana ke nan guda daya da nake tinkaho da shi?” ta tambaya.

Wadanda ake zargi da kashe ‘yar jami’a suka yi farfesu da zuciyarta domin yin tsafin samun kuxi
Wadanda ake zargi da kashe ‘yar jami’a suka yi farfesu da zuciyarta domin yin tsafin samun kuxi

Mahaifiyar ta ce danta ya ci amanarta, don haka tana kira ga duk wani mai matsala ya guji zuwa neman mafita ta irin haka, domin gudun fadawa mugun hannu. Ta ce abu mafi a’ala shi ne, in mutum ya shiga matsala ya roki Allah a dakinsa.

Aminiya ta zanta da mahaifin yarinyar mai suna Dabid Oyedele, a daidai lokacin da yake shigar da bayanansa ga ’yan sanda a ofishin rundunar da ke Eleweron a Abeokuta. Ya fadi cikin shasshekar kuka cewa, wannan lamari abin bakin ciki ne da tashin hankali.

“Yarinyar ’yar lelenmu ce, mun dade ba mu samu haihuwa ba kafin mu same ta. Bayan Allah Ya ba mu ita, mun raine ta, mun ba ta kulawa. Ta yi karatu har matakin jami’a, muna cike da fatar za ta kammala a wannan lokaci ta tafi hidimar kasa, muna alfahari da ita, kasancewar mun samu mace a dangi da ta kammala karatun jami’a; sai ga shi wadansu miyagu sun hallaka ta,” inji shi.

Ya ce a ranar da lamarin zai auku, ranar wata Lahadi, bayan ta ziyarce su sai ta ce za ta koma makaranta, domin ta yi shirin jarrabawarta ta karshe. “A can sai aka kira ta a waya, sai ta ce abokan karatunta ne za ta biya ta wajensu domin su yi nazarin karatun jarrabawar tare. Daga nan ta fita daga gidanmu da ke Mowe a Jihar Ogun, bayan wani lokaci ba mu ji duriyarta ba, ba ta kira mu a waya ta shaida mana ta shiga makaranta ba kuma lambar wayarta ta daina shiga, sai muka je makarantarsu, wato Jami’ar Jihar Legas muka bincika ba ta nan,” inji shi.

“Daga nan na sanar da ’yan sanda, wadanda suka bibiyi lambar wayarta suka gano ta a cocin da ke can wani kungurmin daji a Jihar Osun. Fatata hukuma ta bi mata hakkinta, a hukunta su daidai da laifinsu, domin hakan ya zama darasi ga na baya,” inji shi .

Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Kenneth Ebrimson ya nuna takaicinsa kan faruwar lamarin. Ya ce jahilci ne ke sanya wadansu mutane tunanin cewa za su yi arziki idan sun kashe dan uwansu dan Adam sun yi tsafi da shi. Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin, don su fuskanci hukunci da zarar an kammala bincike.