Da Dumi Dumi

Buhari ba shi da Coronavirus, sai Abba Kyari

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ba ya dauke da Coronavirus

Sakamakon wani gwaji da aka yi ya nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya dauke da cutar Coronavirus.

Sakamakon wani gwaji da aka yi jiya Litinin ya nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya dauke da cutar Coronavirus.

Wata majiya a Fadar Shugaban Kasar ta ce an gudanar da gwajin ne bayan an tabbatar cewa Shugaban Ma’aikatansa, Malam Abba Kyari, ya kamu.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ce ta gudanar da gwajin ranar Litinin.

An yi amanna cewa Malam Abba Kyari ya kamu da cutar ne yayin wata tafiyar aiki zuwa Jamus da Masar, wadanda ke cikin kasashen da cutar ta addaba.

ADVERTISEMENT

An ba da rahoton cewa bayan dawowarsa, babban jami’in ya gana da wasu kusoshi a gwamnati, ciki har da Shugaba Buhari, da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, da wasu ministoci.

A karshen makon jiya ne dai Uwargidan Shugaba Buhari, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta bayar da sanarwa ta shafinta na Twitter cewa daya daga cikin ’ya’yan Shugaban Kasar ta killace kanta bayan ta dawo daga Birtaniya.

Ranar Litinin kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ma ya hau shafinsa na Twiiter inda ya bayyana cewa an tabbatar dansa na dauke da cutar kuma an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada ana jinyarsa.

Zuwa yanzu dai an tabbatar da mutum 40 ne suka kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya, har ma daya daga cikinsu ya riga mu gidan gaskiya ranar Litinin, biyu kuma an sallame su bayan sun warware.

A yunkurin dakile yaduwar cutar ne kuma hukumomi a sassan kasar daban-daban suka haramta tarukan da za su hada mutane fiye da 50, suka kuma bukaci ma’aikatan da ke matakin albashi na 12 zuwa kasa da su yi aiki daga gida.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya