Da Dumi Dumi

Da gaske idan mutum ya kalli mai ciwon ido zai iya dauka?

Da gaske idan mutum ya kalli mai ciwon ido shima zai iya dauka a lokacin?

Amsa: A’a ba a kallo ba ne, a taba mai ciwon ne. Wato idan mai ciwon bai wanke hannayensa ba bayan murtsuka idanunsa aka yi musabiha ta hannu da hannu da shi, aka kuma taba ido da hannun kafin a wanke, to shi ne za a iya dauka. Domin dama kwayoyin cuta ne wadanda ido ba ya ganinsu, walau na bacteria ko na birus, suke sa irin wannan ciwon wanda aka fi sani da apollo. Don haka yawan wanke hannaye da sabulu yana matukar rage yada kwayoyin cuta daga wasu cutar zuwa marasa ita.

Kunnena ke kaikayi sai na yi amfani da audugar ‘cotton bud’ na sosa, sai na tsokano wani abu. Ga shi yanzu ina ji ya ishe ni da ciwo da kaikayi, kuma idan na tashi daga barci sai in ji wani dummm! Kamar na kurumce.

Daga Abbas Amin

Amsa: A’a ai wannan ya zama aikin Baban Giwa, aiki ya kwabe ya zama emergency wato matsalar gaggawa. Lallai ga alama ka fasa gangar kunne wadda wadansu suke cewa dodon kunne, wato ear drum ko kuma ka ji mata ciwo. To amma dai kada ka razana, kada kuma ka sake saka wani abu ko diga wani ruwan magani a cikin kunnen. Ka yi maza ka nemi babban asibiti mafi kusa inda suke da likitocin kunne a duba a ga wace gudunmawa za a ba ka har ya warke.

ADVERTISEMENT

Ni kuma na yi fitsari ne sai na ga kiyashi sun zo kan fitsarin kamar suna sha. To shi ne abin ya tayar min da hankali, don na ji an ce alamun ciwon suga ne.

Daga Aminu M. Baffa

Amsa: Duk da cewa bai kamata a ga suga a fitsarin mai lafiya ba, ba lallai ba ne a ce ciwon suga ne da kai. A wasu lokuta idan watakila ka ci ko ka sha abu mai suga da yawa sosai zai iya sa wa har ta kai ya dan bulla a fitsarinka. Duk da cewa bai kamata a samu haka ba, wasu lokuta idan muka sha abubuwa masu sukari sosai, koda na iya barin wani dan suga kadan ya wuce, musamman idan ba ta da lafiya sosai a daidai wannan lokaci. Amma dai koma  mene ne idan dai ka ga abin ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa, wato kullum sai sha-zumami sun hau fitsarinka, to dole ka je ka yi gwajin ciwon suga.

Maganin rage kiba yana da illa ga jiki ne? Domin ni ina so na rage kiba

Daga Muhibbah S.

Amsa: A likitance an fi so a yawaita motsa jiki a kuma rage cimaka ko sanwa. Idan ana haka za a ga kiba na sauka. Idan hakan bai yi amfani ba, kuma likita ya duba ya tabbatar kibar mai hadari ce sosai, za a iya ba da shawarar yin tiyata ta rage girman ciki, wato wadda ake rage girman tumbi din nan don masu mummunar kiba su rage ci. Kin ga duk a cikin abubuwan da na lissafa dai babu kwayar magani a ciki.

Ni kuma ciwon kai yana matukar damuna. Na je asibiti da kyamis an ba ni magunguna amma har yanzu ba sauki. Mece ce shawara?

Daga Aminu kafur, Katsina

Amsa: Ka san ciwon kan ne akwai abubuwa da dama da za su iya kawo maka shi, don haka ba za a san me ya kawo maka shi ba, idan ba bincike da gwaje-gwaje aka yi maka ba, don ban ji ka ambaci gwaje-gwaje ba. Shawara ita ce ka bar kafur ka ziyarci birni ka samu babban asibiti inda likita zai duba ka ya yi maka aune-aune da gwaje-gwaje har a samo dalilin ciwon kan.

Wadanne abubuwa ke jawo yawan barci ga dan Adam, duk da ya kwanta da wuri amma da safe sai ya ji kamar bai yi ba.

Daga Hassan Roged Gwale

Amsa:  Akwai abubuwa da dama da kan kawo yawan barci. Na farko shi ne shigar kwayoyin cuta na trypanosoma masu sa ciwon barci, sakamakon cizon kudan tsando. Shi wannan kuda daga jikin shanu yake zuko kwayar cutar ya sa wa mutum ta hanyar cizo. Wato ke nan an fi samun matsalar a masu kiwon shanu ko masu harka da shanu. An fi samun ciwon a tsakanin makiyayan kasashe makwabta kamar Kamaru da Kwango.

Kafin yawan barci, sai mutum ya fara jin alamu kamar na zazzabin maleriya wato ciwon kai, ciwon jiki, kasala da ciwon gabobi. Su ma shanu masu dauke da wannan kwayar cuta suna yawan samun barcin. Idan mutum na harka da shanu kamar saye da sayarwa, kuma yana samun irin wadannan alamu da kuma yawan barci, to ya je asibiti a bincika ko matsalar ce, domin akwai magani. Idan kudan ya ciji wata mata mai juna-biyu, kwayar cutar za ta iya bi ta mahaifa ta shiga jinin abin da ke ciki, shi ma ya kamu da cutar ke nan.

Bayan wannan sauran abubuwan da kan kawo yawan barci akwai ciwon kiba da ciwon minshari. Mai ciwon kiba wanda kuma shi ya fiya yin minshari, kullum a cikin barci suke, musamman ma barcin rana, domin ba su cika samu da dare ba sosai. Maganin irin wannan yawan barci shi ne rage kiba.

Sai kuma ciwon damuwa, wanda kan iya sa yawan barci. Shi wannan a kwakwalwa matsalar take. Sa’annan akwai wasu nau’ukan abinci masu bugarwa kamar tsumammen kunu ko fura, sai wasu magunguna na asibiti ko na gargajiya wadanda za su iya sa wannan matsala.

A karshe, akwai yawan shaye-shayen magungunan maye barkatai masu bugarwa, kamar baliyam ko sholisho ko ruwan barasa da dai sauransu.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya