Da Dumi Dumi

Da gaske muke kan aikin lantarki na Mambilla – Ministan Makamashi

Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman
Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman ya bayyana cewa babu kasar da za ta ci gaba idan babu wutar lantarki, sannan ya ce idan an same ta kasa za ta wadatu kuma za a samu ci gaba.

A matsayinka na Ministan Makamashi, me kake yi game da aikin wutar lantarki na Mambilla?

Kamar yadda ka ce, in Allah Ya yarda Shugaba Buhari, ba zai kammala wa’adinsa na biyu ba, sai an fara aikin Mambilla, tunda yake an dan samu jinkiri zai kasance ba za mu kammala a wa’adinmu ba, za a ci karfin aikin tunda masu ba mu filin sun yi an gama komai.

Mun yi magana da Gwamnan Jihar Taraba ya yarda, ya ce mu je mu yi aikin lantarkin, mun ba da kudi mun je mun auna kuma mun ba masu aikin aunawar kudinsu a hannu cewa su je su rike a hannunsu. Wannan shi ne tabbas a harkar Mambila ya zama gaskiya, babu karya a cikinsa in Allah Ya yarda.

Farawar shi ne wuya, kada ka manta kudi ne. Kashi 85 cikin 100 na kudin  za a ba mu ne daga waje, kashi 15 cikin 100 ne za mu bayar, to, idan har an fara bada kudin ne a kasa sunansa an gama.

ADVERTISEMENT

Abin da ya sa ba a fara da wuri ba, Allah ne kadai Ya sani, akwai harkar kotu a ciki wani yana cewa shi ne aka ba kwangilar, wasu kamfanoni suka ce su aka ba, domin me ba a ba shi ba? Irin wadannan ke jawo abubuwa. A  tsaya a yi maganinsa ba a samu an yi ba, sai wannan karon ne muka ce, a tsaya a yi maganin abin.

Amma kun daidaita da su?

Mun daidaita, muna kan magana har yanzu, insha Allahu za mu daidaita. Ina so in tabbatar muku cewa, wannan aikin ba zai tsaya ba. Za a fara kamar yadda muka ce za a fara. Kuma babu kotun da ta ce kada mu fara wannan aiki, an gama maganar sun fahimce mu, har mun ba su tabbas, ku zo mu fara duk abin da ya faru da ku mun dauki nauyi mun yarda.

Za ku biya diyya?

Yanzu haka kudin diyya ya fita, na rubuta wa Shugaban Kasa ya sa hannu, kudin diyya ya fita kudin auna fili ya fita.

Saura a fara aiki ke nan?

Yanzu sun ce in ba su wata daya zuwa biyu kafin su gama aune-aune, masu biya ma za su zo su ma za su dauki wata daya kafin nan kamfani zai zo, shi ke nan a warware komai. Sannan za su zo a fara kawo kaya, za a gyara wurare kamar hanya.

A zagaye-zagayen da ka yi zuwa su Kashimbila da Zungeru, me ka gano?

Eh, suna nan suna aiki, komai na ta tafiya, sun kai sama da rabin aikin, kusan kashi 65 cikin 100, sun yi nisa sosai insha Allah cikin wannan shekara zuwa karshenta abin da suka tabbatar mana ke nan, idan ka je ka gani suna aiki awa 24 kamar yadda na fada maka.

Dan Adam na aiki sama da dubu biyu a wajen, idan ka je Zungeru kuma an riga an karasa, idan ka je wasu wuraren a nan a kan hanya. Duk an yi nisa sai kaddamarwa ya rage a yi, wuta za mu samu isasshiya kafin wannan gwamnati ta sauka. Shi ya sa muka ce idan an kammala aikin gyara da rarraba wutar lantarkin za a samu wadatar wutar lantarkin.

Share