✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da goyon bayan al’umma ta’addanci ke yaduwa – Kwamandan soji

Kwamandan Makarantar Kimiyyar Makamai na Sojojin Ruwa ta Najeriya (NNSAT) da ke garin Kachiya a Jihar Kaduna Riyal Admiral Tanko Yakubu Pani ya ce saken…

Kwamandan Makarantar Kimiyyar Makamai na Sojojin Ruwa ta Najeriya (NNSAT) da ke garin Kachiya a Jihar Kaduna Riyal Admiral Tanko Yakubu Pani ya ce saken da jama’a ke yi da nuna halin ko-in-kula a matsayin abin da kawowa da yaduwar ta’addanci a tsakanin al’umma.

Kwamandan ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata yayin da yake karbar lambar yabo daga masu kishin garin Kachiya da suka kai masa ziyara a barikin saboda kokarinsa wajen dakile ayyukan batagari a  Kudancin Kaduna.

Ya bayyana ayyukan batagari a matsayin barazana ga zaman lafiya, inda ya ce akasarin batagarin na zaune ne a cikin al’umma kuma ana rayuwa tare da su a matsayin ’yan uwa da dangi ko baki, inda ya yi kira ga al’umma su tashi tsaye tare da bai wa dukkan jami’an tsaro hadin kai da goyon baya ta hanyar sanar da su duk labarin da ka iya taimaka musu wajen tsamo bara-gurbi daga mafakarsu.

A karshe ya nuna godiyarsa ga jama’ar da su ka karrama shi tare da shan alwashin kara zage dantse wajen maida garin na Kachiya a matsayin wanda zai kubuta daga ayyukan batagari.

Da yake maida jawabi a madadin wadanda suka karrama Kwamandan, Sakataren Kungiyar Masu Kishin Garin Kachiya, Yusuf Usman ya bayyana gagarumin aikin da Kwamandan ya gudanar wurin tsabtace garin Kachiya daga ayyukan barna.

“Munanan ayyuka da suke ci mana tuwo a kwarya da suka hada da fashi da makami da yin garkuwa da mutane da hare-haren ramuwar gayya da satar shanu yanzu sun yi sauki bisa ga irin dabarun da gwamnati da sauran bangarorin jami’an tsaro ke bullowa da su da suka hada da kafa sansanonin tsaro a wurare masu hadari don tunkarar kalubalen da ya addabi yankin,” inji shi.