✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da jarin kilo 1 na fara tsire amma yanzu ina yanka shanu 7 kullum – Alkasim Suya

Wani mahauci da yake tashen sana’ar sayar da tsire a Gombe Alkasim Suya Spot, ya bayyana cewa ya fara sana’ar tsire da kilo daya ne…

Wani mahauci da yake tashen sana’ar sayar da tsire a Gombe Alkasim Suya Spot, ya bayyana cewa ya fara sana’ar tsire da kilo daya ne na nama amma a yanzu yana yanka shanu bakwai a kowace rana kuma yana da shanu sama da 400 da yake kiwo:

 

Aminiya Alkasim yaya ka fara wannan sana’a da kuma halin da kake ciki yanzu?

Na fara sana’ar tsire da kilon nama daya ina gasawa ina yawon talla, har Allah Ya sa wa sana’ar albarka jarin yana karuwa ya kai ina sayen kilo biyu zuwa uku har na fara karfi ina sayen kilo 30 zuwa 40 ina gasawa da kaina ina talla.

 

Daga jarin kilo 40 nawa ya koma?

Daga kilo 40 sai na fara yanka saniya da kaina, sai wadansu suka rika tsegumin cewa ashe dan tsire zai iya yanka saniya. Lokacin da na fara yanka saniya sai na samu waje na zauna ina ci gaba da sana’ar har Allah Ya sa na rika kara yawan shanun da a yanzu ina iya yanka shanu bakwai a kowace rana kuma naman ba ya kwashe.

 

 Yanzu ga ka a cikin garken shanu da sana’ar ce ka mallake su?

Eh a dalilin sana’ar fawa na mallaki wadannan shanu ina saye ina kiwatawa ne idan na dauki wasu na yanka kafin nan wasu suna kara cikewa kuma a cikinsu nake zabowa nake yankawa a lokacin da suka ci dusa suka koshi saboda ni ba na yanka saniyar da ba ta koshi ba.

 

Shanun ’yan kasa ne ko da na kasashen waje?

Akwai na gida amma mafi yawansu na kasashen waje ne da ake kiransu Imbala marasa kaho. Daga baya ne na fara sayo ’yan gida ina surkawa saboda su ma ana samun masu kyau.

 

Yaushe ka fara wannan kiwo kana yankawa?

Gaskiya na fi shekara hudu rabon da in je kasuwa don sayo saniyar da zan yanka, sai dai in sayo wadanda nake kiwatawa ina dauka a cikinsu ina yankawa.

 

Ka ce kana da shanu sama da 400 da guda nawa ka fara kiwo?

Da saniya guda daya na fara kimanin shekara 30 da suka wuce lokacin ina cikin sana’ar fawa.Sannan abin da na samu a kiwon shanu ba zai lissafu ba domin komai da kake gani a jikin saniya kudi ne idan muka yanka bayan mun sayar da naman hatta kaho da kashinta da kasusuwa duk muna sayarwa ne ka ga kuwa ashe alherin yana da yawa.

 

Ganin ka kafu a sana’ar fawa rassa nawa kake da su?

Alhamdulillahi ina da rassa biyar kuma dukkansu a garin Gombe suke mun bude wani a Jihar Bauchi mai kula da harkokin kasuwancin Allah Ya yi masa rasuwa, sai na rasa wanda zai kula da wajen yadda ya kamata sai muka rufe.

 

Akwai masu raina sana’a mece ce shawararka gare su?

Ni dai sana’ar fawa ce ta haife ni don kakana na biyar ma mahauci ne, mu Hausawa da Fulani muna da raina sana’a domin ci da zuci wajen ganin sai mutum ya yi arziki da wuri.

Kamar yadda na fadi da kilon nama daya na fara har ya kai 40 kuma da kaina nake yankawa in gasa har Allah Ya kaddara na samu wajen zama na fara yanka saniya da kaina.

In da na raina sana’ar da ban kai yadda nake ba yanzu, inda nake yanka shanu bakwai kullum kuma suke karewa. Don haka idan mutum yana sana’a ya rika yin tattali, saboda ba abin da ya fi jari, rashin yin tattali kuskure ne. Shi ne wata rana  za su yi maka  rana domin ko gwamnati ma na yin tattali bare dan kasuwa.

 

Ganin kana gasawa har da kaji su ma kai kake kiwatas u?

Na so in fara kiwonsu sai ya zama akwai dawainiya sai muka fara bai wa matan aure da wadansu ’yan uwa suna kiwatawa a gida muna ba su riba muna saye a wajensu.

 

Yaya batun samun abincin shanun?

Saye muke yi don akalla muna sayen tirela 60 na abincinsu a duk shekara inda muke ajiyewa muna ba su.

 

Tunda ba yawo suke yi ba kamar mutane nawa ne suke cin abinci a wajen?

Muna da ma’aikata guda 30 da kowannensu yana karbar albashin Naira dubu talatin da daya duk wata.

 

Mece ce shawararka ga matasa?

Shawarata ita ce matasa su tashi su nemi sana’a, domin rashin sana’a  na jawo mutuwar zuciya. Idan matashi ba ya da sana’a kullum tunaninsa zai zama wani abu daban saboda da zarar ya ji bai da kudi zai yi tunanin aikata mugun laifi da zai kai rayuwarsa ga hallaka.