✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da jarin Naira dubu 50 na bude kamfanina – Mai SAN Youghut

Alhaji Sunusi Abdullahi Abubakar mai kamfanin madarar yogot na San Youghut, na daya daga cikin wadanda suka samu nasara a harkar kasuwanci, matashi ne mai…

Alhaji Sunusi Abdullahi Abubakar mai kamfanin madarar yogot na San Youghut, na daya daga cikin wadanda suka samu nasara a harkar kasuwanci, matashi ne mai kimanin shekara 40, ya shaida wa Aminiya yadda duk da yana da digiri na biyu daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya gwammace ya gwada harkar yogot maimakon aikin gwamnati inda ya fara harkar da Naira dubu 50, kuma a karshe kwalliya ta biya kudin sabulu:

Yaya aka yi ka shigar harkar yin yogot?
Harkar kasuwanci kamar gadon na yi, na tashi na tarar mahaifina yana kasuwanci, bayan kammala sakandare, mahaifina ya samu matsala a harkar kasuwancinsa abubuwa duk sun dame wannan ya sa a matsayina na babban dansa dole na shiga harkar kasuwancin, na dauki ragamarta duk karatun da na yi a baya na yi ne ina hadawa da kasuwanci. A kullum zan je makarata in dawo in shiga kasuwa, shi ya sa har na gama jami’a ban taba kwana a cikinta ba. Kuma kayan da muke saidawa suna da alaka da sana’ar da nake yi a yanzu, domin dama muna saida abubuwa ne da suka shafi hada sinadarai na abinci da mata suke yi a gida. Tunda a lokacin akwai wuta ba matsala kamar yanzu za ka ga mata suna yin kankara da kayan tsotse-tsotse kamar su askirim da madarar yogot da abubuwa dama da suke da alaka da na’urar firiji. To duk kayan da ake harhada wadannan sinadarai kamar madara da sukari da launi da sauransu, muna sai da su, kuma shagonmu ya shahara a kasuwar, mutane da dama sun san muna sayar da wadannan sinadarai. To da haka na yi hulda da masu yin madarar yogot da kamfanonin da suke sayar da sinadaran. Duk sababbin abubuwan da aka kawo, mu za mu karanta mu rika yi wa masu sana’ar bayani kan yadda za su yi amfani da su, saboda akasarinsu ba Turanci suke ji ba, to wannan sai ya kara taimaka min wajen fahimtar yadda ake yin yogot. Idan masu yin yogot suka samu matsala ni za su kawo wa kukansu kuma ni zan tambayi masu kamfanin su kuma su yi min bayani ko in sake karanta irin takardun da suke yin bayanin yadda suke hada sinadaran, kuma in yi musu bayani har a dace.
To, wannan ya nuna cewa ba ka je makarantar koyon yadda ake hada yogot da kayan tsotse-tsotse ba ke nan?
Wato a gaskiya a kasuwa na koya, abin da na karanta a jami’a ba ya da alaka da harkar madara, sai dai in ce bangare ne na kasuwanci kuma kasuwanci idan ka karanta shi kamar yadda malamammu suka koyar da mu a kowane bangare na rayuwa za ka iya shigar da kanka.
Yaya aka yi ka fara tunanin shigar da kanka cikin yin yogot?
Abin da ya sa na fara tunanin shiga harakar shi ne ganin cewa na kusan gama jami’a kuma da ma na yanke shawarar ba zan yi aikin gwamnati ba, saboda sabo da kasuwanci. Kuma na fahimci akwai wadanda suke samun abinci ta karkashin kasuwancin da muke yi, sai na ga in na bar wurin na ce zan yi aiki, kamar mutane za su tawaya, kuma idan na ce zan ci gaba da kasuwanci kamar yadda mahaifina yake yi har ya shahara, shi kuma nasa na iya samun matsala domin abokan ciniki  ni suka sani, wadanda suke kawo mana kaya, ni suka sani, to ka ga in na ce yanzu na ware shagona, to ai ka ga ba dadi, kamar ina gasa da mahaifina ke nan. To a kan haka ne kawai na ga wadanda suke yin madaran a wancan lokaci ba su da da yawa. Kuma kasancewar madarar da suke yi na da kyau kuma akwai bukatar a zamanantar da yadda suke yi, a yi ta a kan tsari na ilimi. A lokacin duk wadanda suke madarar a Zariya mutanen Lebanon ne ana kiran madarar Hafsa, daga nan aka fara yin iri-iri, sai Kilako, sai kuma Jamil ya fara da sauransu, su ne suka fara yin yogot a Zariya.
A lokacin da ka fara akwai wadanda suka taimaka maka ne?
A gaskiya kusan ni kadai na fara, a lokacin da wani kawuna ganin cewa sakamakon jarrabawar da na samu a jami’a ta yi kyau sosai, sai ya ba ni kyautar kudi saboda nuna jin dadi. To wannan kyauta ita ce farkon jarin da na fara wannan sana’a da ita. A lokacin da ya ba ni kyautar sai na zo na nuna wa mahaifina, bayan ya sa albarka sai ya tambaye ni wace sana’a nake son yi? Sai na ce masa sana’ar yin madarar yogot. Ya ce da wannan kudi na ce, ai idan an kyale ni da su zan fara in Allah Ya sa musu albarka za a kai.
Kudin za su kai nawa domin na ga har ana juyayinsu?
Ya ba ni Naira dubu 50 ne da su na fara.
Yaya ka yi wannan kudi suka saya maka kayan aikin da ka fara sarrafawa?
To wannan kusan shi ne ma labari mai ban sha’awa a cikin al’amarin gaba daya. To, ka ga dai a cikin yanayin yadda ake ciki da ya ba ni kudin ai duk ya gama min komai domin tun nan na fara lissafin yadda zan yi da su, saboda ka ga dai duk mai bukatar ya fara sana’ar yin madara sai ya tanadi abubuwa kamar haka: na farko sai ya nemi na’ura sanyaya kaya firiji, kuma sai an samu abin da za a zuba domin yin tallar madarar ko abin hawa domin yawatawa. To a lokacin sai na sayi keke mai dan kwandon nan guda daya, da ita ce muka fara, sai firiza da kuma madarar da za a fara da sukari da sauran sinadaran hadawa. To dama a gidan da na tare inda na yi aure ni kadai ne kuma akwai daki a gidan sai na gyara a nan na fara. Sai kuma na kama shago inda in an yi za a kai ya zama kamar cibiyarmu; sai kuma na’urar like bakin leda indan mun zuba madarar, ita kuma ledar a kasuwa muke sayo ta, kuma muka yi mata suna muka ba masu bugawa suka yi mana tambari domin likawa a jikin ledar madarar. Kuma da madara kilo biyu muka fara da sukari daga nan kudin suka kare. To da ka muka fara mun sayi madara kilo biyu, sukari kilo daya da sauran sinadarai. Abin like bakin leda mun fara ne da zubawa a leda muna like ta, idan kuma ba wuta, to, sai mu nemo kyandir muna like bakin da shi. Kyandir dai da ake ganin haske da shi, kuma a lokacin nan matata tana taimakawa wajen dafa min ruwan zafi da sauran aikace-aikacen da suka dace da ita, kuma da abin ya fara tafiya, sai ita ma na sa ta a ciki, na ba ta kula da harkar kudi da aje su, har dai abubuwa suka ci gaba da tafiya. Iyalina ta ba da gudunmawa kwarai da gaske wajen tafiyar da al’amarin, domin a wancan lokaci ba ana maganar daukar ma’aikata ba ne tunda ba wani karfi muke da shi ba, ana kokari ne a ga tsaya da kafafu.
To a lokacin bayan ka gama sarrafa madarar kai ne kake dauka a kan keken ko ka samu yaro ne?
A cikin yara unguwarmu da suke zama a bakin rumfarmu da idan an sayi kaya suke kai wa mutane, to cikinsu sai na yi wa daya magana mai suna Aminu Hamisu da shi muka fara. Shi ne in dan an yi yogot din yake dauka a keke yana zagayawa domin talla, wato muna ba shi a kan wani farashi shi kuma ya dora nasa a kai, haka muka yi ta yi da shi kuma ya dore, har zuwa yau, muna tare da shi.
Kasancewar jarin bai ishe ka ba, ta yaya ka rika tara kudi ko kana kaiwa banki ne don bunkasa sana’ar?
Ai lokacin ba maganar kaiwa banki ko asusu ba ne, domin akwai bukatu da yawa a kanmu, na farko da muka fara mun yi da inganci har masu sana’ar suna cewa ai domin ba ina sayen kayan hadin ba ne, a ba ni lokaci kadan za a ga yadda zan koma. To kafin in fara sai da na duba su wa suka fi iya madara mai kyau a Zariya, sannan na ce bari in yi wadda ta fi tasu ko mu zo daidai. To gaskiya a lokacin da muka fara madarar mun samu karbuwa mutanan da suka san ni sai suna cewa ai kila mahaifina yake ba ni kayan da nake hadawa don haka kada wani ya damu a ba ni zuwa wani lokaci kankane, zan daina domin yanzu diban kayan kawai nake yi, shi ya sa nake yin ta da kauri, kuma hakan ya sa na girgiza wadanda suke yin madara a wancan lokacin. Kuma sai madarar ta karbu sosai kullum muka yi sai bukatarta ta karu, kullum sai mun kara yawanta saboda bukatarta, don haka ba mu da wasu kudi da za mu ajiye, sai dai duk kudin da suka zo mu kara jari.
Yaya ka yi tunanin sa mata suna madarar SAN Youghut, kuma da sunan ta fara shiga kasuwa?
Maganar suna alhamdu lillahi dama harkar kasuwanci na karanta a jami’a, don haka duk abin da ya shafi kasuwanci za a koya maka, kuma a duk lokacin da za ka fara wani abu mai kama da wannan za ka yi la’akari da abubuwa da yawa; na farko sunan da in aka fade shi kowa zai iya amincewa da shi. Misali mu da muke rayuwa a kasar nan muna da kabilu da addinai daban-daban, to, yawanci idan ka fito da kaya in ka karkata sunasa da wani addini, sai ka ga zai iya shafar kaya, kuma in ka fito da suna mai wahala, to shi ma matsala ce. Ta haka muka yi tunanin cewa mu sa suna mai sauki, kuma Allah Ya sa dama sunana Sunusi Abdullahi Abubakar sai na dauka daga cikin sunana sai na sa SAN domin ya yi wa mutane saukin fada.
Ina ka kai a sana’ar taka?
Yanzu kusan duk Arewa ana samu, haka jihohin Kudu duk muna kai kaya.
Kana da ma’aikata kamar nawa yanzu?
A gaskiya masu yi mana aiki a halin yanzu za su kai akalla kusan mutum dari da wani abu, ban da diloli da muke ba su kaya a kan farashin sari, kuma abin da zai kara ba ka sha’awa shi ne cikin wadanda muka sa su a cikin harkar kasuwancinmu har da guragu da muka saya musu kekuna irin nasu, kuma muka ba su jarin da za su fara da ita, domin mu hana su yin bara.
Mene ne burinka nan gaba?
Burina a yanzu in Allah Ya sa na kammala sabon kamfaninmu, to za mu hada gwiiwa da Fulani domin su rika samar mana da madarar shanu, har mun fara shirin yin haka.
Ko akwai hannun jarin wasu a cikin kamfaninka?
A’a babu hannu jarin kowa, koma babu bashin banki, sai dai muna tunanin hada hannu nan gaba da masu bukata kuma za mu fara amfani a bankin Jaiz domin ba su hulda da ruwa.
Yanzu karfin jarinka kana zaton zai kai nawa?
A gaskiya ba zan iya sani ba, amma duk abin da ka gani na kamfani ne.
Kana da wata shawara ga gwamnati?
Shawarata ita ce maganar tallafi da ake cewa ana badawa, abin ya zama siyasa kuma idan ka dubi duk inda ake yi, sai ka ga ba wani ci gaban da ake samu da za su gane. Sai a rika ba masu kananan ma’aikatu a raya su su kuma su samar da aikin yi ga matasa. Su kuma matasa kowa ya yi kokari ya samu abin yi, kada ya raina sana’a kowace iri ce, idan ba ta saba wa addini da dokar kasa ba domin tsira da mutunci.