✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sana’ar kera tukwane akwai masu daukan nauyin karatunsu a jami`a da ma iyayen su –Auwal

Muhammadu Auwal Ibrahim shi ne shugaban kungiyar masu sana’ar kirar tukwane na Kasuwar Muchiya Sabon Gari Zariya, jihar Kaduna. A tattaunawar da Aminiya tayi da…

Muhammadu Auwal Ibrahim shi ne shugaban kungiyar masu sana’ar kirar tukwane na Kasuwar Muchiya Sabon Gari Zariya, jihar Kaduna. A tattaunawar da Aminiya tayi da shi, ya bayyana mana yadda aka yi ya zama shugaban kungiyar da yadda suke kera tukwane da sauran abubawan fasaha akalla dubu 2 kullum. Ya kuma ce sana’ar tukwane na taimaka wa iyaye wajen karatun `ya`yansu a jami’o’i da kula da su. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

 

Gabartar mana da kanka?

Sunana Muhammadu Auwal Ibrahim, ni ne shugaban kungiyar masu sana`ar kera tukwane a kasuwar Muchiya, karamar hukumar Sabon Gari.

Ya aka yi ka zama shugaban kungiyar masu wannan sana’ar?

Muhammadu Auwal: Yadda aka yi na zama shugaban wannan kungiyar, ada ni ne mataimakin shugaba, amma da wa’adin wancan shugaban ya kare, bayan ya kammala wa’adinsa ‘yan kungiyar suka bukaci dole nima sai na fito takara, nima in gwada shugabancin kungiyar masu wannan sana’ar. Jama’a da dama sun rinjaye ni tabbas sai na fito wannan takarar, yawancin abubuwan duk yi min aka yi. Zabe ne aka yi da takardun kada kuri`a da komai kamar yadda ake gudanar da zabe. Da ma`aikatan zabe aka zo aka yi komai da kuri`u da komai aka kirga aka tabbatar da sakamakon cewa na ci zabe.

Tsawon wa’adi nawa ne kuke yi na shugabancin wannan kungiya?

Muhammadu Auwal: Adadin zaben shugabannin wannan kungiya shekaru hudu ne.

Masu wannan sana’ar ya suke samun jari?

Muhammadu Auwal: Da farko akwai masu gidaje. Saboda mu ma akwai ma su gidajenmu da suka raine mu muka tashi a hannunsu tun muna kanana, kuma muna yin aiki tare da su har Allah Ya sa muka bude namu da dan abin da muke samu a wurinsu muka bude namu mu ma ga wasu a kasan mu.

Wannan sana’ar gado ka yi ko koya ka yi?

Muhammadu Auwal: Eh, ni na yi gado, amma wasu da dama ba gado suka yi ba, sha’awa ce kawai ta sa suka koyi sana’ar. Saboda mutane da yawa sukan kawo `ya`yansu su bamu su, akan cewa suna so su koyi wannan sana’ar ta hannu.

Wane irin na`ukan tukwane ku ke kerawa?

Muhammadu Auwal: Na’ukan tukwane mu kan yi manya da kanana, da masu kafa da marasa kafa kuma mu kan yi na shafa wato holoko.

Wane irin suna kuke kiran su?

Sunan su kenan da mai kafa da mara kafa amma akwai lamba da ta banbanta su. Kamar daga lamba daya zuwa biyu, da lamba uku zuwa hudu da lamba biyar zuwa shida. Daga nan sai takwas sai 10 daga nan sai 12, sai 16. Sauran sun hada da 20, sai 30, iya abin da muke kerawa kenan a nan kasuwar Muchiya.

A ina kuke samun kayan kera tukwanen?

Muhammadu Auwal: Muna samo su ne daga alminiyom na kondem din motoci sai mu hada da gwangwani irin na maltina. Akwai dillalai da suke kawo mana. Wani lokacin idan abin ya yanke mana har Abuja muke zuwa mu je mu sayo ko kuma a turo mana daga Fatakwal jihar Ribas.

Bayan tukwane sai me kuke kerawa kuma?

Muhammadu Auwal: Mu kan yi tanda ta alminiyom, mu kan yi kujera ta zama, muna yin turmi. Bayan wannan akwai sauran kere-kere da muke amfani da fasahar mu wajen kera su, kamar  irin su almakashi na teloli idan ya balle ana kawo mana, da hannun wuka shima akan kawo mana mu kera, da kuma abin tuyar kwai na mata da abin matse lemo duk muna yin na alminiyom. A cikin masu wannan sana’ar akwai masu kirkiro wata sabuwar fasahar daban inda a wani wajen ba a yi.

A duk rana kuna kera tukwane kamar nawa?

Muhammadu Auwal: Gaskiya, akalla muna kera tukwane da sauran nau`ukan kere-kere, da suka kai dubu 2 kullum.

Kamar mutum nawa ne suke wannan sana’ar a wannan kasuwar?

Muhammadu Auwal: A yanzu haka banda wanda na yaye da magidanta, ina da wanda suke min aiki sun kai sama da mutum 20. Kuma ba ni kadai bane na ke da irin yawan wadannan yaran a wannan kasuwar, akwai irin mu da dama da suke da yara masu yi masu aiki. A yanzu haka wadanda suke aikin wannan sana’ar za su kai 200.

Wane irin kira za ka yi ga matasa da suke jiran gwamnati ta samar masu da aiki?

Muhammadu Auwal: Gaskiya ni kiran da nake yi wa matasa yanzu fa kai ya waye. Ba lokaci ne na ka tsaya ka ce sai ka jira ka samu aikin gwamnati ba, saboda ka kammala makaranta, wannan lokacin ya wuce. Gaskiyar magana shi ne ka tashi ka nemi sana’ar hannu. Kamar mu masu wannan sana`ar, wasu na amfani da ita don cigaban karatunsu. Su kan zo makarantar tasu ta tsaya su cigaba da aikin suna yi suna karatu da wannan sana’ar. Muna da su da yawa wasu ma yanzu karatun digiri suke duk da wannan sana’ar, suna nan da yawa. Wannan sana’ar na taimakawa iyayen yara wajen karatunsu da kula da su. Saboda gaskiya mu sana’ar mu idan yau ka fara zuwa ba za a rasa abin da za a baka ba, kamar na cin abinci da sauransu da kuma dan abin da zaka ajiye.