✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sana’ar mazarkwaila na yi gida na ilimantar da ’ya’yana – Bala Dan Yabe

Malam Bala Dan Yabe Gimi Tasha da ke Karamar Hukumar Makarfi ya kwashe shekara 25 yana sana’ar mazarkwaila a yankin. A tattaunawa da Aminiya a…

Malam Bala Dan Yabe Gimi Tasha da ke Karamar Hukumar Makarfi ya kwashe shekara 25 yana sana’ar mazarkwaila a yankin. A tattaunawa da Aminiya a wajen sana’arsa da ke kauyen Bargi ya bukaci gwamnatin ta tallafa musu da jari domin inganta sana’ar tasu:

Aminiya: Kamar shekaru nawa kake wannan sana’a ta yin mazarkwaila?

Dan Yabe: Ni haifaffen kauyen Bargi ne, amma mazaunin kauyen Gimi Tasha. Na kai shekara 25 ina wannan sana’a domin mun tashi mun tarar da iyayenmu na yi mu ma muka dora har muka janyo kannenmu da ’ya’yanmu cikinta tare muke wannan tafiya.

Sannan a kullum muna ganin fa’idar abin domin a yanzu akalla mutum 15 ke wajen nan suna cin abinci a karkashina.

Aminiya: Kamar katan nawa na mazarkwaila kuke yi kullum?

Dan Yabe: Idan har mun tashi lafiya a kullum muna yin katan 5 in Allah Ya yarda na rawar doki wanda ake kira mazarkwaila. Murhu 10 muke dafawa kuma yana ba mu katan 5 ma’ana ke nan duk murhu 2 yana ba mu katan daya. Da rake muke yin sa wato farin rake. Kuma a shekarun baya da iyayenmu ke yi da doki suke yi amma yanzu zamani ya zo da ci gaba sai muka gano babur. Don haka da babur muke amfani wajen matse ruwan raken.

Wato mu masu karamin karfi ke nan domin akwai masu yi da injin da ke nikawa ko matse ruwan raken. A da mutum ke juyawa yana matse raken daga baya sai aka koma doki yanzu kuma babur da inji ake amfani da su.

Aminiya: Wane kalubale kuke fuskanta a wannan sana’a?

Dan Yabe: Kalubalenmu gaskiya shi ne rashin jari da za mu rika sayen rake saboda masu noma raken nan daban suke sannan masu dafawa daban. Kamar noman damina masu yin sa daban ne. Ka ga muna bukatar jarin da za mu rika noma raken sannan idan ruwa ya dauke mu samu jarin da za mu sayi na rani. Har ruwan sama ya zo.

 Aminiya: Wadansu naganin sana’ar na neman gushewa domin jama’a ba su son yin ta me ya kawo haka?

Dan Yabe: Yawwa! Abin da ke janyo haka shi ne rashin jari domin gwamnati ba ta shigowa cikin harkar tana tallafa mana. Kullum akan sa mana rai amma har yanzu babu taimako. Sai dai kuma zuwan wannan gwamnati ta yanzu muna fatan ta sa hannu a wannan lamari namu. Domin a kullum muna ji a kafafen watsa labarai Shugaban Kasa yana cewa jama’a su rungumi noma, to, muna son ya sani cewa mun kama noman, don haka a taimaka mana a sama mana wata hanya da za mu samu jari wanda kudin ruwan zai kasance  mai sauki da za mu iya biya. Za a iya ba mu jarin da za mu biya a cikin shekara daya domin mu sayi kayan aiki musamman mu sayi rake mu kuma sayi injinanmu na matse raken.

Aminiya: Wane amfani ka samu a tsawon shekarun da ka kwashe kana yin sana’ar?

Dan Yabe: Ni sai hamdala domin ’ya’yana sun yi karatu, ciki akwai ’ya’yana biyu da suka kammala karatun malanta na NCE a yanzu. Da har sun fara koyarwa amma da Allah Ya kawo juyin-juya hali sun bar aikin. Ni kuma na san abincinsu ne ya tsaya amma yanzu sun dawo cikin wannan sana’a muna yi tare. Saboda haka muna bukatar Shugaban Kasa da kuma gwamnatin jiha ta taimake mu da jari. Da wannan sana’a ta mazarkwaila na ilimantar da ’ya’yan nan nawa na kuma yi wa ’ya’yana mata aure haka kuma mazan ma a yanzu biyu sun yi aure. Sannan kowa a cikinsu na yi masa gidansa sai dai mu hadu a nan wajen aiki a yi wasa da dariya a watse.

Aminiya: Batun jari kamar nawa kuke bukata gwamnati ta ba ku domin inganta sana’ar taku?

Dan Yabe: Idan aka ba mu dan jari da ba zai gagare mu ba, zai taimaka mana mu kananan manoma. Jarin da za a iya bamu shi ne kamar na Naira dubu 500 zuwa miliyan daya. Kuma za mu biya cikin shekara daya da yardar Allah. Muddin aka ba mu a kan lokaci.

Aminiya: Wane jan hankali za ka yi ga matasa da ba su son yin sana’a?

Dan Yabe: Wannan ya sa muka kafa wannan dan kamfani nawa muka kuma janyo matasa cewa su sani fa ba za mu jira gwamnati mu ce sai ta ba mu aikin yi ba. Dole sai mun tashi mun taimaki kanmu kafin gwamnati ta kawo mana taimako. Ka dai ga matasa a nan kusan ni kadai ke gaba da su a shekaru ni kuma na koyi wannan abin wajen mahaifina ne kuma yana nan da ransa, sai dai ya manyata yana gida. Kullum yana sa mana albarka tare da ba mu shawarar mu rika taimakon juna da sauran mutane daidai gwargwado. Wadansu ma na zuwa nan neman taimakon ruwan rake musamman masu ciwon hanta. Masu cutar hanta daga Kano da Kaduna na zuwa mu ba su ruwan rake idan sun bukaci biya sai mu ce a’a mu dai fatanmu Allah Ya ba su lafiya. Saboda haka sana’a aba ce mai kyau da matasa za su runguma domin dogaro da kai.