✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sana’ar wankin hula na gina gida –  Malam Hamza

Malam Hamza Muhammed mai sana’ar wankin hula ne a Sabon Garin Tudun Wadan Kaduna, kuma ya ce ya kwashe shekaru sama da 15 yana wannan…

Malam Hamza Muhammed mai sana’ar wankin hula ne a Sabon Garin Tudun Wadan Kaduna, kuma ya ce ya kwashe shekaru sama da 15 yana wannan sana’a wadda ya ce akwai alheri a cikinta. Ya shaida wa Aminiya cewa sana’a ce mai kyau mai kuma saukin yi kuma da ita ya sayi gida:

Aminiya: Shekara nawa kake sana’ar wankin hula?

Malam Hamza: Zan kai shekara 15 da fara wannan sana’a ta wankin hula. Da farko ba wannan sana’a nake yi ba dinkin hula da karatun Alkur’ani nake yi, daga bisani ne na fara wankin hula.

Aminiya: Koyon sana’ar ka yi?

Malam Hamza: A’a ni ban koya ba amma dai na zauna da masu yin sana’ar ce. Suna yi ina kallonsu har ta kai ga ni ma na fara yi. Ga shi har yanzu muna cin abinci da ita.

Aminiya: Me ya ba ka sha’awa ka fara sana’ar?

Malam Hamza: Abin da ya ba ni sha’awa shi ne na lura cewa sana’a ce da ba za ta tsare min komai ba wato ba za ta hana ni nazarin Kur’ani da nake yi a kullum ba.

Aminiya: Da sana’ar hula da kuma dinkin hula wacce ta fi a gare ka?

Malam Hamza: Wankin hula ya fi min rufin asiri fiye da dinkin hula. Domin da wankin hula na gina gida na kuma kara aure bayan na ladan noma da aka yi min.

Aminiya: Ke nan dai sana’ar wankin hula abar dogaro ce?

Malam Hamza: Kwarai da gaske, domin kuwa ba ni da wata sana’a da ta fi wankin hula a yanzu domin ita nake yi har yanzu da ita kuma nake ciyar da iyalina.

Aminiya : A kullum hula nawa kake wankewa?

Malam Hamza: A kullum ina wanke hula 30 zuwa 40. Kuma farashin wankin hular yana kamawa ne daga Naira 150 zuwa 200.

Aminiya: Ta yaya kake gane masu hular kasancewar ba suna kake rubutawa a kan ko wacce hula da aka kawo wanki wajenka ba?

Malam Hamza: Yau da gobe kawai. Gaskiya ne ba na rubuta sunan wanda ya kawo min hula domin ina da baiwar da insha Allahu idan har na taba wanke hula sau daya zuwa biyu zan gane mai hular, na san mai ita.

Wanda kawai ke caza min kwakwalwa shi ne wankin hulunan Sallah domin a lokacin ne bakin ido ke kawo min wanki. Lokacin za ka ga wanda bai taba kawo wanki ba ya kawo baya ga haka kuma a lokacin za ka ga huluna har sama da 150 an kawo wanki. Kuma wasu bakin ido ke kawowa. Amma duk da haka ina kokarin gane masu su.

Aminiya: Sai dai ban ga yara masu koyon sana’a a wajenka ba?

Malam Hamza: Abin da ya kawo hakan shi ne, ni ban raina kadan ba, amma su yaran suna raina kadan.

Aminiya: Ko masu sana’a irin taka na bukatar taimakon gwamnati?

Malam Hamza: Ai ba za mu rasa bukatar taimako ba musamman idan ka yi la’akari da kudin da ake sayar da buhun karo wanda a yanzu akalla buhun karo ya kai Naira dubu 25. Ka ga idan muka samu tallafi daga gwamnati na yadda za a rage mana farashin buhun karo ai zai taimaka mana kwarai da gaske.

Aminiya: Akwai hulunan da sun kwashe shekaru a hannunka ba a zo an karba ba. Me yake kawo haka?

Malam Hamza: Haka ne domin a wasu lokutan masu su ke kawowa daga nan ba za su sake dawowa domin karba ba. Kwanan na dauke wasu na kai wa iyalan wani mutum da ya kawo min wanki amma ban sake ganinsa ba sai labari kawai na ji cewa ya rasu. Yanzu haka akwai huluna da sun kwashe shekara hudu a hannuna ba a zo an karba ba, ni kuma ban san inda masu su suke ba.

Aminiya: To, ya kake yi da irin wadannan huluna da ba a zo an karba ba?

Malam Hamza: Kwanaki na wanke huluna da suka dade a hannu na wasu sun kai shekara hudu kuma ban san masu su ba. Na yi sadaka da su da niyyar Allah Ya kai ladan ga mizanin masu su. Ka ji yadda nake yi da hulunan da suka dade a hannuna.

Aminiya: Wane kira za ka yi ga matasa kan koyon sana’a domin dogaro da kai?

Malam Hamza: Kirana ga matasa shi ne su tashi tsaye su koyi sana’a domin ga shi su sun ki sana’a mu kuma baki mun karbe musu sana’ar  yi. Ka san an ce ma raina kadan barawo ne, don haka mu ba mu raina kadan ba muna yi kuma muna samun abin ciyar da iyalanmu. Saboda haka sana’a abar yi ce gaskiya.