Daily Trust Aminiya - ‘Da sanin mahaifinsu na yi musu cikin shege’
Subscribe

‘Da sanin mahaifinsu na yi musu cikin shege’

Wani matashi da ya yi wa wasu ‘yan mata (Ya da kanwa) fyade har suka dauki ciki ya ce da izinin mahaifinsu ya yi.

Aminiya ta samu rahoto cewa tun sadda yaran masu shekaru 13 da 17 a yanzu suke makarantar firamare matashin da ake zargi ya fara yi musu fyade.

Majiyarmu a ofishin ‘yan sanda ta Ikotun ta a jihar Legas ta ce ‘yan sanda suka cika hannu da wanda ake zargin ne a ranar Litinin, bayan  matsin lambar da mahaifiyar yaran ta yi na a yi musu gwaji wanda ya tabbatar suna dauke da juna biyu.

Da bincike ya yi nisa, sai yaran suka sanar da ‘yan sanda cewar cikin na matashin ne kuma tun suna makarantar firamare yake yi musu fyade.

‘Ya sandan suna ce wanda ake zargin bai musunta ba, amma ya ce da izinin mahaifinsu yake lalata da su.

Hakan ta sa ‘yan sanda damko mahaifin yaran domin ya kare kansa daga zargin hannunsa a fyaden da aka yi wa ‘ya’yan nasa.

Kokarin wakilinmu na ya ji daga bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas, Bala Elkana ya ci tura saboda rashin samun layin wayarsa kuma bai maido masa sakon tes din da ya tura masa ba.

texem
More Stories