✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da umarnin Buhari aka tube Sarki Sanusi II – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da hannu a cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnan Kano ya…

Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da hannu a cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnan Kano ya yi a ranar Litinin.

Kwankwaso, wanda shi ne mutumin da ya nada Sanusi a shekarar 2014, ya ce abin da ya faru a jihar lamari ne “na bakin ciki, wanda duk gwamnati mai daraja ba za ta aikata ba”.

Sanata Kwankwaso, wanda shi ne jagoran ‘yan adawa a Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP ta kasa, ya shaida wa BBC Hausa cewa “shugabannin gwamnati na Kano su da kansu ne ke cewa umarni aka ba su (su tube Sarki Sanusi).

Shi [Buhari ne] ya ba su umarni,” sai dai bai bayar da wasu shaidu da suka tabbatar da hakan ba.

Yunkurin da Aminiya ta yi na jin tabakin fadar shugaban kasa ya ci tura, domin mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, bai amsa sakon da muka tura masa ba kawo yanzu.

Tun bayan da aka cire sarkin da jama’a da dama musamman a shafukan sada zumunta ke ci gaba da yin Allah-wadai da lamarin, tare da zargin gwamnatin tarayya da hannu a cikin batun.

Kuma wasu na ganin rashin fitowar gwamnatin ta bayyana matsayarta ya taimaka wurin karfafa irin wadannan zarge-zarge.

‘Buhari na tsoma baki’

Kwankwaso ya yi zargin cewa sabanin maganganun da makusantan Buhari ke cewa, shugaba Buhari ba ya tsoma baki cikin irin wadannan rigingimu, “sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani (Buhari) yana hargitsa inda yake sa hannu”.

“Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al’amuran jihar Kano”, In ji Kwankwaso. “Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu”.

Tun bayan daga aka cire Sarkin a ranar Litinin, gwamnatin Buhari a hukumance ba ta ce komai ba akan batun. Sai dai a makonnin baya Shugaba Buhari ya ce ba zai saka baki a harkokin cikin gida na jihar Kano ba.

A yanzu haka dai Sarki Sanusi na garin Awe na jihar Nasarawa, kuma a ranar Laraba ne ake saran lauyoyinsa za su shigar da kara domin kalubalantar tilasta masa zama a can da gwamnati ta yi.