✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da wahala mu iya komawa Arewa- Hausawa mazauna Anambra

Hausawan unguwannin Nnewi a jihar Anambra, sun ce abu ne mai wahala su iya barin jihar Anambra su koma yankunan Arewa kamar yadda Kungiyar Dattawan…

Hausawan unguwannin Nnewi a jihar Anambra, sun ce abu ne mai wahala su iya barin jihar Anambra su koma yankunan Arewa kamar yadda Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta sanarwa  manema  labarai a Awka babban birnin jihar.

Sakataren kungiyar Hausawa mazauna Nnewi Sani Suleman, ya ce abu ne mai matukar wahala su iya barin jihar Anambra saboda wasu daga cikin su sun fi shekara 40 a yankin, don haka duk wanda ya sanar da cewa, su bar yankunan da suke su koma Arewa wannan babban kuskure ne.

Wasu daga cikin Hausawan sun bayyanawa manema labarai cewa, tun shekarar 1986 suke zaune a Anambra, lokacin daya ace su tashi su koma Arewa, abu ne mai wahala.