Da Dumi Dumi

Da wane dalili PDP za ta zargi APC a Jihar Bayelsa?

Daya-da-daya ko da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasonjo bai ci ribar wannan mulkin na dimokuradiyya da aka fara a 1999, kamar yadda tsohon Shugaban Kasa Dokta Goodluck Ebele Jonathan ya  ci ribarsa ba. Duk kuwa da kasancewa Cif  Obasonjo, a  1998, yafe masa aka yi sannan aka sako shi daga gidan sarka inda yake zaman daurin rai-da-rai kan laifin yunkurin kifar da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha. Samun wannan ’yanci da Cif Obasonjo ya yi sai kuma masu fada-a-ji na kasar nan suka sanya shi a gaba suka ba shi takarar Shugaban Kasar nan a inuwar Jam’iyyar PDP, inda ya yi mulki na tsawon shekara takwas daga 1999 zuwa 2007.

Shi dai tsohon Shugaban Kasa Jonathan, mukamin farko na siyasa da ya fara danawa, shi ne nada shi mamba a Hukumar Daraktocin Hukumar Raya Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur wato OMPADEC, lokacin gwamnatin Shugaban Kasa Janar Abacha yana malami a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Gwamnatin Jihar Ribas.

A 1998, bayan sojoji sun yi niyyar mika mulki, Dokta Jonathan ya shiga Jam’iyyar PDP, ya kuma yi sa’a ta tsayar da shi Mataimakin dan takarar neman  Gwamnan Jiharsu ta Bayelsa wato  Cif Diepreye Solomon Peter Alaimeyeseigha, inda kuma suka yi nasarar lashe zaben a 1999.

Suna cikin zango na biyu ne sai Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa ta tsige Gwamna Alaimeyeseigha a watan Disamban 2005, wanda a bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan, sai Dokta Jonathan likkafa ta yi gaba ya zama Gwamnan Jihar Bayelsa.

A zabubbukan 2007, har Shugaba Jonathan ya samu takarar neman ci gaba da zama Gwamnan Jihar kwatsam! Sai shugaba Obasonjo da neman TAZARCENSA ya ci tura, ya dauko tsohon Gwamnan Jihar Katsina marigayi Alhaji  Umaru Musa ’Yar’aduwa ya ba shi takarar Shugaban Kasa sannan Dokta Jonatahan a zama mai rufa masa baya.

ADVERTISEMENT

Allah cikin ikonSa da kudirarSa, a watan Afrilun  2010, kusan shekara uku ’Yar’aduwa na kan mulki, sai Allah Ya karbi ransa. Nan ma bisa ga tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki, sai likkafa ta kara yin gaba a kan Dokta Jonathan, inda ya zama Shugaban Kasa. Bayan ya kammala wa’adin shekara daya da ta rage musu, sai kuma ya sake tsayawa takarar Shugabancin Kasa a zaben  2011, wanda ya yi nasara.

Kasancewar yana da damar yin zango na biyu, a shekarar 2015 ma ya sake samun sahalewar jam’iyyarsu ta PDP, na ya yi mata takarar Shugaban Kasa, amma kuma bai yi nasara ba, wanda kuma cikin ruwan sanyi ya karbi kaddara, don ko kara shi da jam’yyarsu ta PDP ba su kai ba don kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ya samu.

Tun daga wancan lokaci tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya koma jiharsa ta Bayelsa ta yadda ba kasafai ake jin duriyarsa ba duk da irin faman da matarsa take ciki a kan zargin halatta kudaden haram a gaban shari’a da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati ta EFCC take tuhumarta.

Amma a kan harkokin siyasar kasar nan musamman a kan batutuwan tafiyar da jam’iyyarsu ta PDP, tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya ci gaba da taka rawar da ta kamata a kasa da jiharsa ta Bayelsa.

Alal misali ya taka gagarumar rawa wajen ganin jiharsa ba ta fada hannun sabuwar jam’iyyar adawa ta APC ba a zaben Gwamnan Jihar da aka yi a daidai irin wannan lokaci a shekarar 2015, duk kuwa da irin guguwar CANJIN da APC ta zo da shi.

Sai ga shi kwatsam! A zaben Gwamnan Jihar Bayelsa da aka gudanar ranar 16 ga wannan wata, Jam’iyyar PDP a karon farko cikin sama da shekara 20 da aka fara wannan mulkin na dimokuradiyya ta fadi warwas a hannun Jam’iyyar APC.

A wancan zabe dan takarar Jam’iyyyar APC Cif Dabid Lyon, da ake wa lakabi da  Zaki a Jihar Bayelsa, shi ya lashe zaben da kuri’a dubu 352 da 552, yayin da abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar, Sanata Dauye Diri wanda Gwamnan Jihar Bayelsa ya tsaya kai-da-fata a cikin ’yan takarar Jam’iyyar PDP 21,  lallai shi jam’iyyar za ta tsayar zaben, ya samu kuri’u dubu 143 da 432.

Faduwar dan takarar PDP ya girgiza ubangidansa na siyasa wato Gwamna Dickson, wanda ya yi ta kukan cewa ba zabe aka yi ba a kan tsarin dimokuradiyya illa fashi aka yi musu da bakin bindiga, bisa ga yadda wai Jam’iyyar APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen tursasawa da kuntata wa masu kada kuri’a.

A gefe daya wadansu na zargin tsohon Shugaban Kasa Jonathan da mukarrabansa da laifin faduwar dan takararsu na PDP, bisa ga wasu abubuwa da ya yi tun bayan zaben fitar-da-gwanin Jam’iyyar PDP da dan takararsa Cif Timi Alaibe bai yi nasara ba.

Rahotanni sun ce tun bayan zaben fitar-da-gwanin, tsohon Shugaban Kasa Jonathan da wadansu daga cikin mukarrabansa, har ma da mahaifiyarsa, sun janye goyon bayansu ga dan takarar Gwamnan na PDP sun koma goyon bayan dan takarar APC Cif Lyon. kai karewa ma  an ji mahaifiyar Jonathan tana yi wa ayarin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC addu’ar Allah Ya ba shi nasara a lokacin da ayarin dan takarar suka kai mata ziyara a gidanta da ke kauyen Otuoke a  Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.

Ta bangaren magoya bayansa tsohon Shugaban Kasa Jonathan a ranar 6 ga  Oktoban da ya gabata  ya ki halartar babban gangamin dan takarasu na PDP. A ranar 10 ga Oktoba ba, tsohon Shugaban Kasar ya kai ziyara  fadar Shugaban Kasa da ke Abuja inda suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari, ganawar da ba komai shugabannin biyu suka tattauna ba amma ana mata fassara a kan zaben Jihar Bayelsa. Bayan nasarar dan takarar APC Cif Lyon, zababben Gwamnan da makarraban jam’iyyarsu ta  APC sun kai ziyarar da aka fassara a zaman ta godiya ce ga tsohon Shugaban Kasa Jonathan, ziyarar da ta kasance wai ba- saban ba “Barawo da sallama.”

Mai karatu, ka iya cewa siyasar ubangida da yaron gidan da ya kawo karfi, kamar yadda aka saba gani tunda aka fara wannan jamhuriyyar, ita ta kai Jam’iyyar PDP ta rasa Jihar Bayelsa a karon farko da dawowar mulkin  dimokuradiyya a 1999 a kasar nan. Ko kusa ba cewa nake an yi sahihin zabe a jihohin Bayelsa da Kogi ba, illa dai lallai ne PDP ta fara bincikar kanta  kafin zargi ko kai karar Jam’iyyar APC.

Da abin da ya faru a Jihar Bayelsa ka iya tambayar yaushe gwamnonin jihohi da sauran wadanda suke jin sun isa a fagen siyasar kasar nan za su rika bari dimokruadiyya tana amsa sunanta?

 

Share