Search
Subscribe
Da wasan dabe na fara shiga fim – Musa Kalla

Musa Kalla

Da wasan dabe na fara shiga fim – Musa Kalla

Aminiya ta zanta da dan wasan barkwanci Malam Musa Alasan wanda aka fi sani da Musa Kalla, inda ya bayyana yadda ya fara shiga cikin harkar wasan kwaikwayo da sauran batutuwa:

Yaushe ka fara harkar fim?

Akalla na kai shekara 20 a cikin wannan harka. Amma na fara ne da wasan dabe kafin in dawo ina yin wasan kwaikwayo na talabijin. Na fara ne a Gidan Talabijin na Jihar Kaduna (KSTB), inda suka gayyace mu muka gwada yin wani wasan kwaikwayo mai suna  ‘Mai Dokar Barci’. Bayan wannan wasa na gwaji, Allah cikin ikonSa da tashar ta fara aiki gadan-gadan sai suka kirkiro wani wasan kwaikwayo mai suna ‘Sawun Keke’.

A lokacin Ashiru Sani Bazanga shi ne shugaban gudanar da shirin wanda kuma dama yakan zo ya kalli wasan da kungiyarmu ta dirama take yi sai ya zo a cikinmu ya zabi mutum hudu zuwa biyar wato da Cinnaka da Kwano da ni da Allah Ya jikan rai Tandu da kuma wata yarinya ’Yar Baba. To ka ji yadda aka yi na fara wasan da ake nunawa a talabijin.

Game da su kuma wasannin da ake kira da suna fina-finan Hausa, ba zan manta ba, bayan an kammala fim din Wasila kashi na farko, wata rana sai aka kira ni ta hanyar wani abokina wanda soja ne a yanzu a lokacin za a yi wani fim mai suna Daula wanda har yanzu ma bai fito ba. A lokacin da aka sanya ni gaba aka sanya mini kyamara, take sai mutanen da ba su taba ganina ba suka ga irin yadda na yi kokari kuma suka yaba. Haka shi ma wanda ya bada umarni a wannan fim din wato Is’hak Sidi Is’hak ya yaba mini sosai. Daga nan kuma sai Allah Ya sanya muka fahimci juna da shi ta yadda daga wannan lokaci idan ya shigo Kaduna sai ya kira ni ya fada mini cewa Kallah zo za ka yi min aiki kaza.

To ana cikin haka ka san komai da sila, sai Allah cikin ikonSa Ya maido da Adam A. Zango, Kaduna. Da ya dawo ban san shi ba, bai san ni ba, wata rana sai na aka kira ni a waya, da na daga sai na tambaya da wa nake magana? Sai ya fada mini cewa sunana Adam A. Zango. Sannan ya ci gaba cewa Kallah ina son za ka yi mini aiki.

Na sake tambayarsa yaushe ne? Shi kuma ya fada mini ranar. Ba zan manta ba aikin da na fara yi masa shi ne na fitowa a cikin wata wakarsa mai suna Wazobiya wacce na fito a matsayin maroki shi kuma Sani Idris Moda  Allah Ya kara masa lafiya ya fito a matsayin sarki. To tun daga wannan lokaci Allah Ya hada ni da Adamu wanda ya zuwa yanzu kashi 90 na ayyukansa duk sai ka gan ni a cikinsu.

Me ya ba ka sha’awa ka fara wasan dabe?

Na fara sha’awar yin wasan kwaikwayo tun ina Makarantar Sakandare ta Kurmin Mashi. Don haka a lokacin da muka gama makaranta muna zaman jiran sakamako sai na fara yin wasan dabe.

Ko ka san yawan fina-finan da ka yi?

Gaskiya in na fada maka yawan fina-finan da na fito a cikinsu to kuwa na yi maka karya. Amma dai zan iya tuna da dama daga cikinsu. Akwai irin su Sarki da Namamajo wanda na fito mahaifin Ibro da shi kansa Adam Zangon akwai fim din Abdallah wanda na fito boka. A bangaren wasannin barkwanci kuma akwai su Salula wanda muka yi ni da Daushe da Mai Arziki wanda ni da Ibro ne a cikinsa, akwai irin su Ga Zara Ga Wata da dai sauransu.

Daga cikin fina-finanka wanne ne ka fi so?

Gaskiya duk fim din da na yi ina sonsa. Dalili kuwa shi ne ni dan wasa ne kirana ake yi don in aiwatar da wasa.

To a tsakanin fim din santimental da na camama wane ka fi son yi?

To ni a wurina kusan duk daya ne, abin da ya sanya na fadi haka shi ne, ka ga ni zan iya juya maka fim din barkwanci ya zama na santimental haka kuma zan iya juya labarin fim din camama ya koma na santimental.

Tunda yake ka keto zamani biyu ko yaya za ka kwatanta wancan lokaci da kuka fara yin wasan fim da yadda ake yin sa yanzu?

Gaskiya akwai bambanci da dama ta bangaren abubuwa da yawa. Domin mu da muna wasan kwaikwayo ne da kuma fim don neman suna ba don neman kudi ba. Don ba zan manta ba akwai lokacin da nake aiki a Capital TB, Naira 300 ake biyana a wata ina yi musu wasan kwaikwayo. Sannan a da mu sau da dama mu ne za mu dauki nauyin kanmu zuwa wajen da ake daukar fim, kama daga biyan kudin mota da na abincinmu da wurin kwananmu. Amma ka ga yanzu ai duk ana yi ne saboda kudi. Domin yanzu ni ko uwarmu daya ubanmu daya da kai, in dai za a dauke ni zuwa aiki sai ka cake mini kudin motata da na abinci da kuma na wurin kwana kafin kuma daga karshe ka ba ni kudin aikin da na yi. Domin haka ne zai sanya ka daraja sana’ata.

To ta bangaren tarbiyya fa?

To har ga Allah nan ma fa akwai bambanci. To sai dai wani abu daya da nake so ka sani ita fa tarbiyya a gida take farawa kuma a nan ake samar da ita. Yanzu haka a garin nan akwai yaran da ba ’yan fim ba, amma da za ka ji irin ta’asar da suke aiwatarwa ko kare ba zai ci ba. Don haka ya danganta da yadda mutum ya riki sana’ar da kuma irin asalin tarbiyarsa. Yana da kyau kuma ka sani ita nishadantarwa ba tana nufin wasu ayyuka na bata tarbiyya ba ne. Domin yanzu misali a ce Shugaban Kasa ya halarci wani babban taro ka lura da kyau daga farkon taron sai an sanya malami ya bude taro da addu’a sannan a sanya fasto shi ma ya yi tasa addu’ar, kana daga bisani kuma sai ka ji an ce masu koroso su fito su nishadantar da mahalarta taron. Shin abin tambaya a nan su masu koroson nan da suke hade maza da mata kuma suka zo a gaban manyan baki maza da mata ciki har da malaman nan suka tiki rawa kowa na kallo sun bata musu tarbiyya ne?

Wace shawara za ka ba matasa masu irin sana’arka?

Shawarata a gare su ita ce su rike sana’ar da gaske. Domin duk yadda ka dauki abu a haka zai kasance maka. Kai ko da gwal kake sayarwa a kasuwa idan dai ka dauki sana’ar da wasa haka za ka kare ba ka tsinana komai ba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin