Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Da wuya Ronaldo ya buga wasansu da Ajad

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

A ranar Talatar da ta wuce ce kulob din Jubentus na Italiya ya ce da wuya shahararren dan kwallonsa Cristiano Ronaldo ya murmure har ya buga wasan da kungiyar za ta yi da kulob din Ajad na Holand a ranar Laraba mai zuwa a gasar Zakarun Turai zagayen Kwata-Fainal.

Ronaldo wanda yake jinya bayan raunin da ya samu a cinyarsa, an ce yana fatan ya murmure don ya buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Ajad din.

ADVERTISEMENT

Kimanin mako biyu ke nan rabon da Ronaldo ya buga kwallo sakamakon raunin da ya ji lokacin da yake yi wa kasar haihuwarsa Portugal kwallo.

Nan gaba kadan ake sa ran Ronaldo zai murmure don ci gaba da wasa.

ADVERTISEMENT