✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da wuya Shirin Shege-Ka-Fasa ya yi tasiri a Arewa – Mukhtar Abubakar

An bayyana cewa kafa kungiyar tsaro ta Shege-Ka-Fasa da wadansu matasan Arewa suka yi don mayar da martani kan yadda gwamnonin Kudu maso Yamma suka…

An bayyana cewa kafa kungiyar tsaro ta Shege-Ka-Fasa da wadansu matasan Arewa suka yi don mayar da martani kan yadda gwamnonin Kudu maso Yamma suka kafa kungiyar tsaro ta Amatekun ba za ta yi tasiri ba kuma za ta kai labari ba, saboda rashin hadin kan mutumin Arewa da kuma rashin kishi irin nasa.

Alhaji Mukhtar Ahmad Abubakar, wani dan Arewa mazaunin Kalaba a Jihar Kuros Ribas ya bayyana haka yayin zantawa da Aminiya a Kalaba, inda ya ce, “Batun shirin zai yi tasiri ko ba zai yi ba sai dai mu yi addu’a Allah Ya sa. Amma babu alamar haka. Dalilin da ya sa na ce haka, ba sabon abu ba ne, rashin kishi ne kafa kungiya makamanciya irin wannan a Arewa don wadanda aka kafa yawanci ba su yi tasiri ba.”

Ya ce rashin hadin kan ’yan Arewa shi zai sa rashin tasirin kafa kungiyar.

Wata matsala da Alhaji Mukhtar Ahmad Abubakar ya ce tana ci wa mutanen Arewa tuwo a kwarya ita ce, “Akwai abokan zaman Arewa a kasar nan sun fi ’yan Arewa da mutanenta kishin junansu da kuma bangaren kabilu ko yanki. “Misali kabilun Kudu maso Gabas, da na Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Kudu, suna son junansu suna kishin junansu mu kuwa abin ba haka yake ba,” inji shi.

“Ba mu da kishin junanmu ba mu da hadin kai a junanmu, idan ma an ce a hada kai kowa tunaninsa yadda zai gyara kansa zai yi kawai, ko kuma yadda za a ce shi ne wane kurum. Babu akidar a ce bari a taimaka wa yanki ko wani mutumin yanki,” inji shi.

Sai ya ce, “Shawarata a nan ita ce idan za a yi gaskiya, jama’armu su duba su ga abokan zamansu a bangarorin kasar nan, yaya suke yi, su yi koyi. Su yi kishi da wannan sannan al’amarin su zai cimma nasara.”