Da Dumi Dumi

Da ya gaji mahaifinsa a Majalisar Wakilai a Jigawa

Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa
Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa

Da ya gaji mahaifinsa a  Majalisar Wakilai bayan ya lashe zaben cike-gurbi a karkashin Jam’iyyar APC. Dan takarar na APC,  Malam Musa Muhammad Adamu Fagen Gawo ya gaji mahaifinsa marigayi dan Majalisar Wakilai Alhaji Muhammad Adamu Fagen Gawo wanda ya rasu yana kan kujerar a watannin baya.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) reshen Jihar Jigawa ta bayyana cewa Musa Adamu Fagen Gawo ya lashe zaben da aka yi a Mazabar Babura /Garki a Majalisar Wakilai a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Wakilin hukumar zabe a Karamar Hukumar Babura, Malam Ahmad Kaugama ne ya karanta sakamakon zaben a karamar hukumar inda ya shaida wa manema labarai cewa Alhaji Musa Muhammad Adamu Fagen Gawo ya samu nasarar lashe zaben ne da kuri’a dubu 48 da 318 yayin da abokin karawarsa Malam Nasiru Garba Dantiye na Jami’yyar PDP ya sha kasa da kuri’a dubu 24 da 135, sai Malam Bashir Umar na Jami’yyar ADP ya samu kuri’a 458 wadda shi ne ya zo na uku a zaben.

Wadansu magoya bayan Jam’iyyar PDP da ke Karamar Hukumar Babura, sun yi korafin cewa gwamnati ta yi musu kama-karya wajen dora masu wanda ba sa so a kan kujerar Majalisar Wakilan.

Sai dai a bangaren Jam’iyyar APC, magoya bayanta sun ce zargin kama-karya ko dauki-dora a  zaben da ’ya’yan Jam’iyyar PDP suka yi babu kanshin gaskiya a ciki, illa dai ’yan adawar suna fadin haka ne saboda  zafin kayen da suka sha.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda wakilinmu ya gane wa idonsa an gudanar da zaben cikin kwanciyar  hankali. Sai dai a wasu wuraren musamman a garin Babura ba a samu fitar mutane da yawa zuwa wajen zaben ba.

Amma a yankunan karkara an samu fitar mutane sosai zuwa wajen zaben, sannan su raka su jira har aka bayyana sakamakon zaben.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya