✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da yawa daga cikin tsofaffin ’yan kwallon Najeriya ni na horar da su -Lawan Basko

Alhaji Lawan Abdullahi da aka fi sani da Lawan Basko shi ne mai horar da kungiyar kwallon kafa ta KKD da ke Tudun Wada Kaduna. …

Alhaji Lawan Basko, Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta KKD da ke Tudun Wada KadunaAlhaji Lawan Abdullahi da aka fi sani da Lawan Basko shi ne mai horar da kungiyar kwallon kafa ta KKD da ke Tudun Wada Kaduna.  Ya bayyana ma’anar KKD da yadda kulob din ya samo asali da shekarunsa da nasarori da kalubalen da ya fuskanta da wasu batutuwa tun daga wancan lokaci kawo yanzu.  Wakilinmu Ahmed Garba Mohammed ya samu nasarar zantawa da shi kuma ga yadda hirar tasu ta kaya:

Zan so in san cikakken sunanka?
Sunana Alhaji Lawan Abdullahi amma wanda aka fi sanina da shi a harkar kwallo shi ne Lawan Basko.
Me ya sa ake kiranka da Lawan Basko, shi Baskon dan kwallo ne?
A’a, a gaskiya ba sunan dan kwallo ba ne, don tun kafin in fara harkar kwallo aka rada mini wannan suna.  Akwai wani direba wanda soja ne ana kiransa dan mai gyada shi ya fara kirana da wannan suna (Basko) tun kafin in fara harkar kwallo.  Wannan abu kuma ya faru ne kimanin shekara 40 da suka gabata. Kamar da wasa haka sunan ya rika bi na har yanzu.
Ka yi karatun zamani?
A gaskiya ban yi karatun zamani ba, amma dai na yi na allo amma daga baya na dan taba karatun yaki da jahilci kuma duk da haka ban yi nisa a karatun ba saboda hidimar neman abincin yau da kullum, don haka zan iya cewa ban yi nisa ba.
Yaya aka yi ka fara kocin wannan kungiyar kwallon kafa mai suna KKD da ke Tudun Wada Kaduna kasancewa ba ka yi karatun zamani ba sannan ba ka mallaki shaidar horar da kwallo ba?
Da farko dai ba ni ne kocin kungiyar na farko ba, na karbi ragamar ce daga wajen wasu.  A da, a lokacin da ’yan wasan suke tafiya harkar kwallo sukan yi korafin ana gallaza musu, a wasu lokuta ma akan hana su yin wasan kwallo saboda an fi karfinsu ganin haka sai suka shaida mini a matsayi na na matashi mai jini a jika a wancan lokaci.  Daga lokacin ne na yanke shawarar binsu duk inda za su je wasa don idan ana ganin irinmu a wurin watakila ba za a yi musu komai ba.   To tun daga wancan lokaci ne sai suka fahimci ina bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban kulob din a fannoni da dama, daga nan aka yanke shawarar ba ni ragamar kulob din gaba daya.  To sannu a hankali na rika tafiyar da harkar kulob din tare da wadansu da ke kusa da ni wadanda suka rika ba ni shawarwarin da na rika samun nasara.  Kafin ka ce kwabo na samu nasarori ta hanyar lashe kofuna kuma nan da nan kulob din ya yi suna sannan ni ma na yi suna a yankin Tudun Wada da Jiha da ma kasa baki daya.  Duk da ba ni da shaidar horarwa na samu kwarewar da kowace irin kungiyar kwallo aka ba ni zan iya horar da ita ba tare da an samu matsala ba.  Hasalima ko kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles aka ba ni, zan iya horar da ita.  Abin da ya sa na fada maka haka shi ne ai da yawa daga cikin tsofaffin kungiyar kwallon kafa ta kasa sun taba yin wasa a karkashina, irin su Daniel Amokachi da dahiru Sadi da Garba Lawal da sauransu.  To tun daga wancan lokaci kawo yanzu da tsufa ya fara kama ni, ni ne shugaban kulob din kwallon kafa na KKD.   Sai dai a ’yan shekarun baya ne na raba kulob din gida biyu, watau akwai KKD ta manya da kuma ta yara.  Yayin da nake shugabantar ta manya, Muhammadu Wokas shi ne shugaban kulob din a matakin na yara a halin yanzu.
To mene ne ma’anar KKD?
A gaskiya ni ma na zo kulob din ne na tarar ana kiransa da sunan KKD, ba ni na rada masa ba.  Amma dai an shaida min abin da ake nufi da KKD shi ne KADUNA KICK AND DIE.  Don haka tun daga wancan lokaci har yanzu sunan da ake kiran wannan fitaccen kulob da ke yankin Tudun Wada Kaduna kenan.
Wane irin nasarori kulob din KKD ya samu?
Ya samu nasarori masu dimbin yawa, don mun lashe kofuna da ba zan iya lissafa maka su da kai a dan kankanen lokaci ba.  Mun lashe kofuna a ciki da wajen Jihar Kaduna da ma a kasa baki daya.
Wane kalubale kulob din yake fuskanta?
Babban kalubalen da kulob din ke fuskanta shi ne na rashin kudi, don babu wani tallafin da muke samu daga wajen wani ko wasu ko gwamnati in ban da abin da ba a rasa ba daga wajen tsofaffin ’yan kwallonmu da suka yi fice da kuma dan abin da muke tarawa a tsakaninmu don gudanar da kulob din.
Za ka iya lissafa mana fitattun ’yan kwallon da suka buga wa kungiyar KKD kuma suka yi fice a kasa da duniya baki daya?
kwarai da gaske.  Akwai shahararrun ’yna kwallon da suka yi suna a ciki da kuma wajen Najeriya da suka taba yin kwallo a kulob din KKD.  Akwai irin su dahiru Sadi da Taju Olaiya da Daniel Amokachi da Garba Lawal da Tajudeen Onyekami da Abdullahi Heyman da Kabiru Afto da sauransu.  Kai zan iya cewa da yawa daga cikin ’yan kwallon Green Eagles ko Super Eagles sun taba yin wasa a kulob din KKD.
Wace irin nasara ka samu a harkar kwallo?
A gaskiya a yanzu haka ba zan iya kididdige maka irin nasarorin da na samu a harkar kwallo ba.  Kadan daga ciki shi ne irin sunan da na yi a Jihar Kaduna da ma kasa baki daya.  Duk inda ka je za ka ji ana kiran Lawan Basko, wasu ma ban san su ba.
To wane irin tallafi kuka samu daga wajen tsofaffin ’yan kwallon kulob din KKD irin su Daniel Amokachi da Garba Lawal da sauransu?
A gaskiya kowane daga cikinsu ya yi bakin kokarinsa a wajen tallafa mana da kudi da kuma kayayyakin wasanni.  Da yawa daga cikinsu sukan kawo mana kayayyakin wasanni da suka hada da kwallaye da rigunan wasa da wanduna da takalma da kudi da sauransu.  Kuma har yanzu da yawa daga ciki idan sun shigo kasar nan tare muke yin atisaye a filinmu da ke Tudun Wada Kaduna, ka ga zan iya ce maka har yau muna tare da su.
To akwai wani kaso da kuke samu ne idan dan kwallonku ya samu kulob a kasa ko kuma a kasashen waje abin da ake kira Commission?
Gaskiya ba mu taba samun ko kwabo idan wani dan kwallonmu ya samu kulob a wsni wuri ba.  Ka san akwai bambancin yadda ake gudanar da harkar kwallo a da da kuma a yanzu.  A da kwallon kawai ake yi ba tare da an bi wadansu ka’idoji a rubuce a inda kulob zai yi yarjejeniya da dan kwallo ba.   Watakila da a wannan zamani ne, to da mun bullo da tsarin duk dan wasan da wani kulob zai dauka daga wajen mu sai ya ajiye mana wani kaso (commission) amma mu ai kamar wahala muka yi a baya, mun horar da ’yan kwallo masu yawa amma haka suka tafi aka bar mu ba ko kwabo.  Sai dai watakila mu canza tsarin a nan gaba.
Ka taba fita wata kasar ketare a harkar kwallo?
A gaskiya ban taba fita ba, amma akwai lokacin da aka yi yunkurin fitar da ni amma abin bai yiwuwa ba.
Mene ne burinka ga wannan kungiya ta KKD a halin yanzu?
Babban burina shi ne kungiyar ta cigaba da samun daukaka a kasa da kuma a ketare.  Sannan ina fata za a samu shugabannin da za su cigaba da tafiyar da harkokinta ko bayan na daina harkar kwallo a nan gaba.
Yaushe aka kafa KKD?
Kulob din KKD ya fi shekara 40 da kafuwa.  Hasalima zan iya ce maka shi ne kulob na farko da aka fara yi a yankin Tudun Wada.
Yaya bambancin kwallo a  zamanin da, da kuma yanzu?
Akwai bambanci, ‘yan kwallon da sun fi mayar da hankali don madarar kwallon suke yi amma na yanzu hankalinsu ya fi karkata ga neman kudi.
Wace shawara za ka ba matasan ’yan kwallo na yanzu?
Shawara ta gare su ita ce su dauki harkar kwallo tamkar sana’a wacce za su riketa hannu bibbiyu.  Yau harkar kwallo ta zama abin alfahari a duniya ba ma a kasar nan kadai ba.  Harka ce da ake samun arziki a dan kankane lokaci amma fa idan sun mayar da hankali.
Ita kuma Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF wace shawara za ka ba ta?
Ta rika shiga kowane lungu da sako na kasar nan don ganin ta zakulo matasan ’yan kwallo a kulob-kulob da ke Unguwanni alal misali kamar a kulob din mu na KKD da ke Tudun Wada Kaduna da sauransu, hakan shi zai sa a rika zakulo matasan ’yan kwallon da kasar nan za ta yi alfahari da su.
Yaya harkar iyali?
Ina da mata da ’ya’ya har da jikoki.
Na gode da wannan hira.
Ni ma na gode, Allah Ya kara daukaka jaridar Aminiya ta kamfanin Daily Trust. A gaskiya muna alfahari da wannan jarida mai tarin albarka da kuma farin jini.