Da Dumi Dumi

Daba wa ciki wuka da Yari ya yi

A makonnin baya ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’azeez Yari,  ya yi kirari ya daba wa cikinsa wuka a kokarin da yake yi na ganin gwamnatin Jihar Zamfara ta biya shi abin da ya kira ‘hakkokinsa.’

Shi dai tsohon Gwamna Yari ya aika wa Gwamna mai ci ne wata takarda da yake bukatar gwamnati ta biya shi wasu hakkokinsa da suka kunshi fanshonsa da wani alawus na Naira miliyan 10 da ake ba shi duk wata, wadanda ya ce tun bayan saukarsa daga mulkin jihar na wata biyu kawai aka biya shi, saboda haka yana bukatar gwamnati ta biya shi hakkinsa har da na watannin baya.

Alhaji Abdul’Azeez Yari dai ya canja dokar biyan fansho na tsofaffin gwamnoni da mataimakinsu ta jihar ce watanni kadan kafin saukarsa daga mulkin jihar,  inda Majalisar Dokokin Jihar ta amince da sabuwar dokar da a rika biyan tsohon Gwamnan cikakken albashin Gwamna a matsayin fansho na tsawon rayuwarsa, sannan a rika ba shi Naira miliyan 10 duk wata a matsayin alawus, kuma za a gina masa gida a duk inda yake so, sannan a saya masa motoci guda biyu, wadanda za a canja masa duk bayan shekara hudu, haka kuma za a dauki nauyin lafiyarsa da ta iyalansa tare da zuwa hutu na wata guda duk shekara.

Shi ma Mataimakin Gwamna da Shugaban Majalisar Dokikin Jihar da Mataimakinsa akwai tanadin da aka yi musu kwatankwacin matsayin kowannensu.

Abin mamaki ne a ce ana irin wannan son kai a jiha irin ta Zamfara, jihar da take kan gaba wajen dabbaka shari’ar Musulunci a kasar nan,  domin kuwa ko a lokacin da Shugaba Buhari ya je jihar domin yakin neman zabe a zaben da ya gabata, lokacin da tsohon Gwamna da tsohon Gwamna Yari suka hau dirom domin yin jawabi da kabbarori suka fara.

ADVERTISEMENT

Amma abin mamaki sai ga shi tsohon Gwamna Yari ya sanya an yi dokar da za ta sanya a rika ba shi miliyoyin Naira duk wata a matsayin fansho da alawus, alhali an bar tsofaffin ma’aikata ba a biya su fanshonsu ba, duk da cewa cikin cokali ne.

Masu fashin-baki na ganin tsohon Gwamna Yari ya tara wa kansa garabasa ce saboda yana ganin shi ne zai ci gaba da juya akalar gwamnatin Jihar Zamfara, domin tun daga dan takarar Gwamna har zuwa ’yan Majalisar Tarayya da ta jihar duk sai dai ya tabbatar masu yi masa biyayya ne aka tsayar a APC. Wannan matakin da ya dauka ne ya jawo masa matsala tare da Jam’iyyar APC, domin Kotun Koli ta rushe zaben duk ’yan takarar Jam’iyyar APC na jihar.

A matsayin Yari na mutum mai kaunar shari’ar Musulunci, kamata ya yi ya nuna misali ta hanyar guje wa dukiyar Jihar Zamfara, ya ce shi ba zai karbi fansho ba saboda akwai ma’aikata da suka bauta wa jihar na tsawon shekara 35  amma ana biyan su abin da ba ya kashe kishi kuma ba a biya a kan lokaci.

Kuma kamata ya yi ya ce tunda shi zai tafi Majalisar Dattawa ba ya bukatar kudin Jihar Zamfara domin za a rika biyansa a inda zai koma, amma sai ya bari hadama ta rinjaye shi, inda yake so ya rika karbar makudan kudi a jiharsa kuma ya je Majalisar Dattawa yana karbar wasu makudan kudin.

A ka’ida an ce Gwamna ba ya bukatar ya taba ko kwabo a albashinsa, komai gwamnati ta dauke masa har sai ya sauka daga mulki, an yi haka ne domin a kawar da shi daga wata sha’awa da za ta sanya ya wawure dukiyar gwamnati, amma duk da haka sai ga tsohon Gwamna Yari yana ta kokarin tara dukiya ta hanyar gwamnati kuma an ce wai shari’a ake yi. Haba jama’a!!!

Ga dukkan alamu alhaki ne ya kama tsohon Gwamna Yari har ya rubuta waccan takarda da ya tona wa kansa asiri ya kuma tona wa sauran tsofaffin gwamnoni asiri, domin da ya yi shiru ya bi ta karkashin kasa da haka ba ta faru ba, wato soke biyan wannan garabasa da ya so a rika biyansa.

Wannan abu da ya faru dai ya nuna cewa ba Jihar Zamfara da al’ummarta ce a gaban su Yari ba, aljihunansu kawai suke so su cika. Idan ba haka ba, ta yaya za a fito da wannan tsarin mai wahala da zai yi saurin durkusar da tattalin arzikin jiha komai karfinsa, balle tattalin arzikin jaririyar jihar irin Zamfara.

Lallai Gwamna Matawalle ya kyauta da ya rufe ido ya soke dokar, bai kawar da kai ya bar ta ba tunda shi ma nan gaba zai shiga sahun masu karbar garabasar.

Babu shakka hakan da Gwamna da ’yan majalisa suka yi shi ne daidai, domin idan aka bar dokar za ta durkusar da jihar ce gaba daya, komai ya tsaya cik.

Ba banza ce ta sanya wadansu gwamnonin suke tabbatar da cewa wadanda suka amince da su ne kawai suke maye gurbinsu a gwamnati kuma suke zama ’yan majalisa saboda su rika juya su yadda suke so, idan kuma wani ya yi tutsu a tsige shi. Saboda haka ne ake tursasa wa masu kwadayi suke yi abin da Gwamna ke so komai illarsa ga jama’a. Amma wani dan majalisar ya gwammace ya rasa kujerarsa da ya yi abin da zai cutar da jama’a.

Wannan abu da ya faru a Zamfara ya kamata ya zama darasi ga wadanda giyar mulki ke bugar da su har su rika ganin sai abin da suke so ne kawai za a yi, kuma babu wanda ya isa ya fada musu gaskiya su saurare shi. ‘Girman kai rawanin tsiya,’  inji Hausawa.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya