✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Kasafta Ribar Kasuwanci (2)

Na fara bayanin yadda dan kasuwa zai kasafta ribar da ya samu daga harkarsa ta kasuwa a matsayin dabarar kasuwanci a kasidar da na gabatar…

Naira2-178x300Na fara bayanin yadda dan kasuwa zai kasafta ribar da ya samu daga harkarsa ta kasuwa a matsayin dabarar kasuwanci a kasidar da na gabatar a makon da ya gabata. A kasidar ta baya, na yi nuni ga dan kasuwa cewa babbar dabara ce gareshi  da ya ware wani kaso na ribar da ya samu domin kara karfin jarinsa. Kason da dan kasuwa zai ware daga cikin ribarsa domin inganta jarinsa zai kasance daidai da bukatarsa ta yin haka. Na ce idan jarin dan kasuwa na da girma idan ya kwatanta da irin harkar da ya ke yi, da kuma bukatar jarinta, to ba zai ware wani kaso mai girma ba daga ribarsa domin kara karfin jarinsa ba; haka kuma dan kasuwa na iya ware kaso mai yawa daga ribarsa domin kara yawan jarin da ya ke juyawa idan jarin nasa ba shi da karfi sosai.
Shawara ta biyu akan kasafta ribar kasuwanci da na ba dan  kasuwa ita ce ta ware wani kaso daga ribarsa domin inganta ko misaya ko sabunta kadarar da ya ke juya jarinsa da ita. Na musalta wannan shawara da kasancewar harkoki da yawa na bukatar motoci domin tafiyar da su, kamar gidan bulo da gidan burodi da ko kuma kasancewar dan kasuwa babba ko matsakaicin mai harkar kayan masarufi, irin su shinkafa da sukari da sauransu, inda dan kasuwa zai bukaci mallakar motocin daukowa da kaiwa wuraren da ya sayi wadannan kayayyaki, ko ma’ajiyarsu, ko kuma kaiwa wadanda suka sayi kayan a wajensa.
Na kuma yi gargadi da jan hankali a kasidar cewa ware kudi daga cikin ribar kasuwanci domin sabunta ko musaya motoci da injina da sauran kayayyakin tafiyar da harka ya zama dole domin a kullum karfinsu karewa yake yi yayin da ake anfani da su wajen tafiyar da harkar. Na kuma jaddada hakan inda na nuna  muhimmanci al’amarin, domin rashin yin hakan zai kasance ya dan kasuwa a mawuyacin hali yayin da wadannan ababen aiki suka kasa, ba shi kuma da sukunin sayen wasu. Sai na yi alkawarin karin bayani da kuma fito da sauran shiyyoyin da ke bukatar amfana da kasafin ribar kasuwanci, a wannan makon. dan kasuwa ware kudin da zai gyara motoci ko injinan da ya ke amfani da su wajen tafiyar da harkokinsa. Zai kuma yi hakan ne ta hanyar kiyasta irin gyaran da zai yi musu a shekara ko a watannin gaba. Misali, sai dan kasuwa mai sayar da kayan masarufi ya sayi mota akori-kura sabuwa domin hidimar harkarsa, sai ya yi mata babbar inshora (comprehensibe), inda zai biya kudi mai dan yawa, fiye da na karamar inshora (wato Third Party da makamantan su). To sai kuma ya hasashi irin gyara da sabis da zai yi mata a wannan tsakanin: Abin lura anan sabuwar mota ba za ta bukaci gyara mai yawa a shekara farko ba. Misali, idan dan kasuwa ya ware Naira dubu 10 a shekarar motar ta farko, to sai ya ajiye mata dubu 15 a shekara ta biyu, ya kuma ware dubu 20 a shekara ta uku. Haka zai ta yi har sai ya sabunta ta.
To, sai kuma ware kudin sabunta motar, wanda da Turanci ake cewa ‘Depreciation’.  Kamar yadda na yi bayani a baya, kowacce mota kuma kowanne inji da ake amfani da da shi, na samun raguwar karfi a kullum, saboda haka tsarin sabunta shi ya zama dole. dan kasuwa zai kiyasta shekarun da motar da zai yi amfani da ita za ta yi kafin karfinta ya kare. karewar karfin mota ko na inji na kasancewa yayin da ta tsufa ko injin ya tsufa ya kasance kullum cikin gyara, ana ta kashe mata kudi kuma ba a samun isasshen biyan bukata daga motar ko daga injin kamar yadda aka saba samu a baya. Zan dora daga nan idan Allah Ya kaimu mako na gaba. Barka da Sallah.