✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Kasafta Ribar Kasuwanci (4)

A kashi na hudu na wannan makala ta Kasafta Ribar Kasuwanci zan dora a kan inda na tsaya a makon da ya gabata, da na…

A kashi na hudu na wannan makala ta Kasafta Ribar Kasuwanci zan dora a kan inda na tsaya a makon da ya gabata, da na yi alkawarin karasa bayani da misalta yadda dan kasuwa zai yi amfani da kiyasi ya kasafta ribar kasuwanci domin ware kudin sabunta kayan gudanar da harkarsa; zan kuma yi bayani a kan abin da dan kasuwa zai ware daga ribarsa ta kasuwanci domin bukatar kansa, da kuma wanda zai kasafta domin ‘ko- ta- kwana’.
 Kafin dan kasuwa ya ware wani kaso daga ribarsa ta kasuwanci domin bukatar kansa sai ya fara la’akari da bukatar da harkarsa ke da ita, musamman ma ta inganta jarinsa, ko bukatar fadada, harkarsa kamar yadda na yi bayani a kashi na biyu na wannan makala. Zai kuma ware duk hakkin hukuma da ya san lokacin bayar da  shi yazo, ko ya kusa. Wadannan hakkoki na hukuma sun haca da haraji da kudaden sabunta lasisi da kudin wuta da na ruwa da sauransu.
dan kasuwa zai kuma ware kudi don inganta kayan aikinsa da suka kama daga motoci zuwa injina, kamar yadda na yi bayani a makon jiya. Sai kuma kudin sabunta wadannan kayan aiki (wato Depreciation) da na yi bayani a makalar baya da kuma zan yi bayanin yadda za a yi kiyasin fidda su a nan. To akwai hanyoyi kamar hudu da ake wannan kiyasi, amma zan yi bayanin kiyasi mafi sauki a nan domin dan kasuwa ya fahimta ya aiwatar da kansa ba tare da ya tuntubi Akanta ba. Ana ce da wannan kiyasi ‘Straight line method’, ga kuma yadda ake yi: dan kasuwa zai raba kudin da ya sayi kadarar da zai warewa wannan kudi da yawan shekarun rayuwarta, sai ya ware wannan kudi daga ribarsa ya ajiye a cikin wadannan shekarun rayuwar wannan kadara.
Idan mai karatu bai manta ba, na yi bayanin yadda zai kiyasta shekarun kadarar da ya saya domin tafiyar da harkarsa, walau mota ko wani injin tafiyar da harkarsa. Misalin yin wannan kiyasi na ware kudin sabunta kadara shi ne, mu kaddara cewa dan kasuwa ya sayi motar tafiyar da harkokinsa a kan Naira dubu 100, sai ya kiyasta shekarun rayuwarta cewa shekara biyar ne. To sai ya raba Naira dubu 100 da shekara biyar na rayuwar wannan mota, inda zai samu Naira dubu 20. Wato zai rika ware Naira dubu 20 a kowace shekara ke nan domin sabunta wannan motar. Saboda haka a duk sa’in da ya kasafta ribarsa sai ya ware wannan kudi domin wannan bukata; wato idan shekara-shekara yake lissafin harkarsa, sai ya ware Naira dubu 20, idan wata shida-shida yake lissafi, sai ya ware Naira dubu goma duk sa’in da ya yi lissafi. Idan kuma bayan ko wane wata uku yake lissafi, sai ya rika ware Naira dubu biyar a kowane lissafinsa.
  To, ba lallai ba ne dan kasuwa ya ajiye wannan kudi a wani banki, ko a wani asusu yana kallonsu ba, yana iya juya su, walau a cikin harkar da yake yi, ko kuma a wata harkar da ya san ba ta da hadarin asara mai yawa, kuma wacce zai saka wa ido sosai domin gudun hakan. Idan dan kasuwa na juya wannan kudin, sai ya kudurta a zuciyarsa cewa kamar aron su ya yi ba wani bangaren jarinsa ba ne, domin ya riga ya ware su domin wata bukata ta gaba. Yana iya amfani da ribar da ya samu daga wannan kudin, zai kuma cike gibin faduwar da ya samu daga cikinsu yayin da yake juya su daga ribar da ya samu daga ribar jarin da yake juyawa.                    
 Zan yi karin bayani in kuma yi misali a kan hakan idan Allah Ya kai mu mako na gaba inda zan duba kason ‘ko-ta-kwana’ da wanda dan kasuwa zai ware domin bukatar kansa.