✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Kasafta Ribar Kasuwanci (5)

A wannan makon, wanda shi ne mako na biyar da nake bayani a kan yadda dan kasuwa zai kasafta ribarsa ta kasuwanci, zan kammala wannan…

A wannan makon, wanda shi ne mako na biyar da nake bayani a kan yadda dan kasuwa zai kasafta ribarsa ta kasuwanci, zan kammala wannan makala. Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata, a kashi na hudu na wannan makala, na yi bayani da misalai a kan yadda dan kasuwa zai yi amfani da kiyasi ya kasafta ribar kasuwanci domin ware kudin sabunta kayan gudanar da harkarsa. A karshen makalar na yi alkawarin zan yi bayani a kan abin da dan kasuwa zai ware daga ribarsa ta kasuwanci domin bukatar kansa, da kuma wanda zai kasafta domin ‘ko- ta- kwana’. Na kuma yi bayanin yadda dan kasuwa zai ware wannan kaso, da kuma yadda zai iya juya wannan kudi da ya kasafta daga ribarsa, a lokacin da yake tara su kafin lokacin da zai sabunta kadararsa.                    
    Shi kuwa kason ‘ko-ta-kwana’ shi ne kason da dan kasuwa zai ware domin tasowar wata matsala da bai yi tsammanin tasowarta ba.Saboda haka wannan kason ne zai yi amfani da shi wajen magance wannan matsala ba tare da ya tafi neman bashi ko wani tallafi daga banki ko wata kafa ba. Misali, canjin fasaha ko wani tsari na zamani na iya tasowa da zai iya sa wa dan kasuwa ya bukaci wani kudi a wani lokacin da bai shirya ba domin kasancewa ya cimma daidaiton wannan zamanin. A wani misalin, an wayi gari gwamnati ta yi dokar takaice yawan kudin da za a iya fitarwa daga banki. Wani lokaci kuma kamfanoni da sauran abokan hulda na iya fitowa da wadansu ka’idoji da suke bukatar a bi domin cigaba da hulda da su, inda zartar da wadannan ka’idoji zai iya bukatar kudin da dan kasuwa bai tanade su ba. Haka kuma wadansu sababbin abokan hulda na iya zuwa da wata ka’ida da za su bukaci a cika kafin fara hulda da su.
   Yanayi irin wadanda na bayyana a sama na iya kasancewa kamar haka: Wani kamfani da dan kasuwa ke hulda da shi, kamar kamfanin fulawa, na iya cewa ba zai ci gaba da hulda da duk abokin huldarsa da ba shi da motar daukar kaya ba. Ko kuma wani sabon kamfanin taliya ya ce duk dan kasuwar da ke bukatar fara hulda da su sai ya tanadi suto na ajiyar kayansu. To irin wadannan bukatu na iya tasowa dan kasuwa kwatsam ba tare da ya shirya ba. Saboda haka ya zama dole dan kasuwa ya ware wani kaso daga cikin ribarsa domin wannan bukata ta ko-ta-kwana. Kuma dan kasuwa zai iya juya wannan kudi da ya ware ta yadda na ba shi shawarar ya juya na sabunta kadararsa a makon da ya gabata.
    Ware wani kaso daga ribar kasuwanci domin bukatar dan kasuwa ta kashin kansa kuwa zai kasance kaso na karshe da zai ware, domin wannan kamar rara ce daga cikin ribar. Kada mai karatu ya manta shawarar wannan fili cewa a kullu-yaumin dan kasuwa ya kasance mai ware wa kansa albashi daga cinikinsa. Ita kuwa riba ana isa gareta ne bayan an debe duk wahalhalun da dan kasuwa ya yi wa harkarsa, wanda ya hada da albashinsa da na sauran ma’aikatansa. Wannan ya nuna cewa dan kasuwa bai dogara da wannan kaso domin tafiyar da rayuwarsa ba.
Wannan tsari gaba daya na nuna cewa idan dan kasuwa ya bi shi, ya kamanta tafiyar da shi zai samu habakar jarinsa, da samun karo daga tabarbarewar jarinsa. Sannan kuma dan kasuwa zai iya samun karo daga matsalolin da ka iya bijiro wa harkarsa yayin da ya yi mata tanajin ko- ta- kwana daga cikin ribar da yake samu.