✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Kasafta Ribar Kasuwanci

A wannan makon ne zan cika alkawarin da na yi na duba Dabarar Kasuwanci akan yadda dan kasuwa zai kasafta ribar da ya samu daga…

Kasuwar kayan marmari a ZubaA wannan makon ne zan cika alkawarin da na yi na duba Dabarar Kasuwanci akan yadda dan kasuwa zai kasafta ribar da ya samu daga tafiyar da harkarsa. Kamar makalar da na gabatar a makonni biyu da su ka wuce, wato makalar ‘Ko ka na biyan kanka kuwa?’ Wannan makalar ma za ta ba dan kasuwa mamaki.
Da yawa daga ‘yan kasuwa masu karanta wanna shafi, musamman ma kananan yan kasuwa, za su yi mamakin yadda dan kasuwa zai tsaya ya na kasafta ribarsa da ya samu daga cikin harkarsa ta kasuwanci. Wannan mamaki kuwa na iya tasowa ne daga al’adar karamin dan kasuwa na yin hidimar gabansa da dukkanin ribar da ya samu, mafi yawancin irin wadannan ‘yan kasuwa ma ba sa yin lissafin kudin harkarsu daga lokaci zuwa lokaci domin gano ribar da su ka samu, kamar yadda na ke ta jaddadawa a wannan shafin.  
Zan yi bayanin akan kasafin ribar kasuwanci a bisa bayanai da kira da na yi a baya na akan dan kasuwa ya rika yin lissafin ribar da ya samu daga harkarsa ta kasuwanci daga lokaci zuwa loka; misali, kamar ko wata-wata, ko kuma wata uku-uku, ko wata shida-shida, ko kuma sau daya a shekara. Na kuma bayar da shawarwarin yadda za a iya yin hakan, sannan na bayar da mahimmancin yin hakan, musamman ma domin sanin matsayi da kuma yadda harkar tasa ta ke gudana – Ya san ko ya na cin riba, ko ba ya ci, ko kuma ribar da ya ke ci ta kai daidai da wacce ya kamata jarinsa ya ci ko ta gaza hakan.
To a duk lokacin dad an kasuwa ya kasance ya yi lissafin harkarsa ya ga ya samu riba, to akwai bukatar ya kasafta wannan riba ta sa yadda za ta amfane shi a cikin hidimonisa na gaba. Wannan kasafi yan kasuwa na yinsa ta fanni daban-daban, da ya danganta da bukatar harkar, da yanayinta da kuma girmanta. To, akwai wasu abubuwa na kasafin ribar kasuwanci da ke kasancewa a kusan kowacce harka. Misali, kusan ko wacce harka, komin girmanta kuma komin kankantarta, tan a bukatar a inganta jarinta. Saboda haka babbar dabara ce ga dan kasuwa ya ware wani kaso na ribar da ya samu domin kara karfin jarinsa. Kason da dan kasuwa zai ware daga cikin ribarsa domin inganta jarinsa zai kasance daidai da bukatarsa ta yin haka. Idan jarin dan kasuwa na da girma idan ya kwatanta da irin harkar da ya ke yi, da kuma bukatar jarinta, to ba zai ware wani kaso mai girma ba daga ribarsa domin kara karfin jarinsa ba. Akasin haka kuma zai sa dan kasuwa ya ware kso mai yawa daga ribarsa domin kara yawan jarin da ya ke juyawa.
dan kasuwa kuma na ware wani kaso daga ribarsa domin inganta ko musaya ko sabunta kadarar da ya ke juya jarinsa da ita. Misali harkoki da yawa na bukatar motoci domin tafiyar da su, misali kamar gidan bulo da makamantansu. Wasu na bukatar injina domin gudanar da su, kamar gidajen burodi da ire-iren su. Saboda haka ya zama dole a ware musu wani kaso daga cikin ribar da aka samu domin gyaran su, da kuma shirin canja su a gaba, domin a kullum karfinsu karewa yak e yi yayin da ake anfani da su wajen tafiyar da harkar.
Yin hakan na da mahimmanci kwarai da gaske, domin rashin yin hakan zai kasance dan kasuwa ya samu kansa a yanayin da motocin ko injinan sun mutu ba tare da ya shirya sayen wasu ba. Zan kara bayani akan wannan sannan kuma in yi bayani akan sauran kafofin da ya kamata dan kasuwa ya kasafta ribarsa ya zuba musu, in Allah Ya kai mu mako na gaba.